Bayan Dan Wani Lokaci a Tsare, ’Yan Sanda Sun Saki Mataimakin Shugaban APC Na Edo

Bayan Dan Wani Lokaci a Tsare, ’Yan Sanda Sun Saki Mataimakin Shugaban APC Na Edo

  • Bayan shafe wasu awanni a hannun 'yan sanda, an sako mataimakin shugaban jam'iyyar APC a jihar Edo da ke Kudanci
  • An kama Emperor Jarret Tenebe ne a ranar Alhamis da sanyin safiya bisa wasu abubuwan da ba a bayyana ba
  • Ya zuwa yanzu, rahotanni basu bayyana gaskiyar dalilin kama shi ba, amma ana kyautata zaton kama shi na da alaka da gwamantin jihar

Jihar Ebonyi - 'Yan sanda sun sako mataimakin shugaban jam'iyyar APC na jihar Edo, Emperor Jarret Tenebe da aka kama da sanyin safiyar ranar Alhamis.

An gano an saki Tenebe ne daga hannun 'yan sanda da misalin karfe 10:30 na safe bisa umarnin kwamishinan 'yan sandan jihar, Tribune Online ta ruwaito.

Yadda aka sako mataimakin shugaban APC a Edo
Tasiwarar jihar Edo da ke Kudancin Najeriya | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

APC ta sanar da sakin jigonta

Da ake sanar da sako shi, ma'ajin jam'iyyar APC a jhar, Kwamared Ahmed Ekekhide Mahmud ya ce:

Kara karanta wannan

2023: 'Yan Daba Sun Halaka Jigon PDP Kuma Kansila, Ɗan Majalisar Tarayya Ya Sha da Kyar

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na jiha Emperor Jarret Tenebe da aka kama da safiya bisa umarnin mataimakin gwamnan jihar Edo Kwamared Philip Shaibu ya samu 'yanci da misalin karfe 10:30 na safe a yau 16 ga watan Maris 2023 bisa umarnin kwamishinan 'yan sanda."

Rahoton jaridar Leadership an kama mataimakin shugaban na APC ne a karamar hukumar Etsako West da ke jihar, amma dai ba a bayyana dalilin kama shi ba.

Alakarsa ta rikici da mataimakin gwamnan jihar

Tenebe wani babban dan siyasa ne da ke tallata jam'iyyar APC a jihar, kuma ya kasance na hannun daman tsohon gwamna Adams Oshiomole.

A baya, ya zargi mataimakin gwamnan jihar da aikata ba daidai ba a wani bidiyon da ya yadu a kafar sada zumunta.

An kama mutane bakwai da zargin kisan basaraken jihar Ebonyi

Kara karanta wannan

Shugaban Yan Sanda Ya Ba da Babban Umarni, Yace a Takaita Zirga-Zirgan Ababen Hawa Ranar Zaɓe

A wani labarin, kunji yadda aka kama wasu mutum bakwai da ake zargin sun kashe fitaccen basaraken Ebonyi da ke Kudancin Najeriya.

A cewar rahoto, a baya an ayyana neman dan takarar gwamnan jam'iyyar APGA bisa zargin yana da hannu a wannan mummunan kisa da aka yiwa basarake a jihar.

Rahoton ya kuma ce, ya zuwa yanzu dai ana ci gaba da bincike da samun bayanai masu muhimmanci daga mutane bakwai din da suka shiga hannun 'yan sanda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel