Emefiele Ya Shiga Sabuwar Matsala Kan Rashin Umurtar Bankuna Su Rika Biya Da Karbar Tsaffin Kudi

Emefiele Ya Shiga Sabuwar Matsala Kan Rashin Umurtar Bankuna Su Rika Biya Da Karbar Tsaffin Kudi

  • An zargi Mr Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin kasa CBN da kin bin umurnin kotu
  • Zargin na zuwa ne bayan kotun koli ta ayyana halasta kashe tsaffin takardun naira har zuwa ranar 31 ga watan Disamba
  • Amma, ba a riga an aiwatar da wannan umurnin kotun kolin ba don Emefiele bai wa bankuna umurnin fara biya da karbar tsaffin naira ba

An zargi gwamnan babban bankin kasa, CBN, Godwin Emefiele da aikata laifin rashin bin umurnin kotu saboda gazawarsa na bin umurnin kotun koli.

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, babban kotun na kasa, a baya ta yanke hukuncin cewa tsaffin N200, N500 da N1,000 har yanzu halatattun kudi ne har zuwa ranar 31 ga watan Disamba kuma a cigaba da kashe su tare da sabbin kudin.

Kara karanta wannan

Ku Cigaba da Harkokinku da tsaffin N500 da N1000, Kakakin CBN ya yi magana

Emefiele
Emefiele na tashe saboda tsarin sauya sabbin takardun naira
Asali: Getty Images

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan umurnin na kotun koli, har yanzu Gwamna Emefiele bai riga ya bawa bankuna umurnin su rika karba da kuma biyan kwastomomin tsaffin kudin ba.

Gogaggen Farfesa na shari'a Itse Sagay, a wurin taron manema labarai a ranar 8 ga watan Laraba, 8 ga watan Maris, ya ce:

"Kowane dan kasa har da gwamnati da hukumomin ta da shugaban kasa ya kamata su bi umurnin kotun koli.
"Kawai dai babu abin da za a iya yi idan Shugaban kasa bai bi umurnin ba saboda kariya da ya ke da shi, amma doka ta ce ya bi umurnin."
Farfesa Sagay ya ce CBN, karkashin doka, ba ta bukatar umurni daga kowa, har ma shugaban kasa kafin ta bi umurnin kotun koli.

Ya ce:

"Don haka, idan CBN bai riga ya umurci bankuna su bi dokar kotun koli ba, hakan na nufin Gwamna Emefiele yana kin bin umurnin kotu kuma akwai hukuncin yin haka."

Kara karanta wannan

Kashe tsoffin Naira: CBN ya yi maganar da kowa ya kamata ya sani kan hukuncin kotu

CBN ya yi magana a yayin da bankuna suka fara biyan tsaffin naira, kwastomomi sun koka

A bangare guda, babban bankin kasa, CBN, ya yi magana yayin da bankuna suka fara biyan tsaffin takardun naira.

Akwai rudani kan halascin tsaffin N1000 da N500 duk da umurnin da kotun koli ta bada.

Bankuna sun fara biyan mutane da tsaffin kudaden duk da cewa mafi yawan mutane ba su karba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel