“Shekarunta Nawa?” Bidiyon Karamar Yarinya Tana Tuka Tuwo Cike Da Kwarewa Ya Bar Mutane Baki Bude

“Shekarunta Nawa?” Bidiyon Karamar Yarinya Tana Tuka Tuwo Cike Da Kwarewa Ya Bar Mutane Baki Bude

  • Masu amfani da TikTok sun jinjinawa wata karamar yarinya wacce ke tuka tuwo a kan wuta cike da kwarewa kamar wata babba
  • A wani bidiyo da ya yadu, yarinyar ta dauki ragamar kula da girkin kamar wata uwa sannan ta tuke tuwon cikin iyawa
  • Wadanda suka yi martani ga bidiyon sun tun tuna lokacin da suke yara, cewa suma sun yi irin haka

Wani bidiyo da ya yadu a TikTok ya nuno wata karamar yarinya tana hada girkin abinci kamar dai wata babba.

A dan gajeren bidiyon da @lakomelove ya wallafa, an gano karamar yarinyar zaune a gaban murhu tana hada-hadar hada girkin abinci.

Karamar yarinya tana tuka tuwo
“Shekarunta Nawa?” Bidiyon Karamar Yarinya Tana Tuka Tuwo Cike Da Kwarewa Ya Bar Mutane Baki Bude Hoto: @lakomelove.
Asali: TikTok

Yarinyar na ta tuka tuwonta daga cikin tukunyar da ke zaune a kan murhu hankali kwance cike da kwarewa.

Tana ta amfani da muciya wajen duba tuwon daga lokaci zuwa lokaci kuma ta tuke shi tsaf cikin kazar-kazar.

Kara karanta wannan

Ali Ya Ga Ali: Bidiyon Yadda Budurwa Ta Yi Kicibis Da Iyayenta a “Go Slow” Tana Gaggawa Ta Koma Gida Don Ta Yi Dare a Waje

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ana haka ne, wani ya zube daga tukunyan. A hankali ta kwashe sannan ta mayar da shi cikin tukunyar.

Yadda take rike muciyan ya nuna cewa ta kware kuma lallai an yi mata tarbiya mai kyau.

A halin da ake ciki, mutane da dama sun yi martani a manhajar ta TikTok inda suka jinjinawa yarinyar.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@user7621178289667 ya ce:

"Amma sai ka samu budurwa yar kwalisa mai shekaru 30. Ban iya girki ba. Wannan za a yi mace tagari a gaba."

@bea wa papa ta ce:

"Sai a Afrika kawai. Ina alfahari da kasancewata yar Afrika. An yi mana horo mai kyau ciki da waje."

@maurineonditi ya tambaya:

"Shekarunta nawa idan zan iya tambaya? Aiki ya yi kyau."

@anitakleinhans71 ta yi martani:

"Diyata shekarunta 26, uwa ce ammna ko shinkafa bata iya dafawa ba, Allah madaukakin sarki ya albarkaci hannunki, diyata."

Kara karanta wannan

Yadda Hankalin Wata Mata Ya Tashi Gamida Dugunzuma Saboda Kama Diyarta da Wani a Otel.

Yaro ya bige da bacci bayan ya yi wa iyayensa barna

A wani lamari na daban, jama'a sun cika da mamaki bayan cin karo da bidiyon wani karamin yaro da ya zauna ya shanyewa iyayensa milo da suka ajiye don shan shayi.

Bayan yaron ya dirka wanda ya yi masa, sai kawai ya bingire da bacci a wajen yayin da hannunsa ke cikin gwangwanin milon.

Asali: Legit.ng

Online view pixel