Tsakanin Hukumar Hisban Jihar Kano Da Matasa Yan TikTok

Tsakanin Hukumar Hisban Jihar Kano Da Matasa Yan TikTok

  • Hukumar Hisba ta shiga tsakanin Mubarak Isa Muhammad da Nazifi Bala Muhammad da kuma Gwabnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje.
  • Murja Ibrahim Kunya da abokanta guda Ashiru Mai Wushirya, Aminu Ibrahim BBC da Sadik Sharif Umar uku an cilla su gidan gyaran hali na satittika, tare da umartar su shara.
  • Hukumar Hisba ta kama wani waishi Al-Amin G-Fresh akan wasa da sallah a cikin vidiyon sa na TikTok, tayi masa ƙwalkwabo tare da aika sa Islamiyya.

A ƴan Kwanakin nan an samu balahira tsakanin ƴan TikTok da kuma hukumar hisba dake rajin ganin an samu tarbiyya irin ta addinin musulunci a jihar Kano.

Hakan tasa da yawa daga cikin su suka baƙunci bayan kanta, gidan cin gabza da gidan gyaran hali. A yayin da wasu suka sha bulala, da kuma tara haɗi da horon shara.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Mayaƙan Boko Haram Tsagin ISWAP Sun Sheƙe Masunta 26 A Borno

Ƴan TikTok kamar su Sadiya Haruna, Mubarak Unique Pikin, Murja Ibrahim Kunya kaɗan ne daga cikin irin wadannan mutane.

Kunya
Tsakanin Hukumar Hisban Jihar Kano Da Matasa Yan TikTok Hoto: Facebook.com/swaganism
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shin Me Yasa Hisba Ke Musu Kamun Kazar Kuku ne?

Kano dai kamar yadda aka santa, jiha ce mai bin tafarkin addinin Muslunci.

To amma halayyar mafi yawa daga cikin masu yin TikTok na sabawa da addinin na Islama ne da kuma al'adun mutanen jihar.

Sukan wallafa bidiyon su a Manhajar ne ba tare da kula da al'adu ko addinin mutanen jihar ba.

Abin yakai ga zagin shugabanni, yiwa mutane barazana tare da bata tarbiyyar matasa dake kallon wannan kafa a matsayin wani waje dake da tasiri a rayuwar su.

Hakan ce tasa hukumar ta Hisba take gayyatar ƴan TikTok ɗin akan wallafa irin wadannan vidiyon da suka saɓawa addinin musulunci tunda suna da mabiya miliyoyi.

Kara karanta wannan

Saura kiris zaben gwamna: Sojoji sun kama katin zabe 1,671 da takardun aikin zabe a wata jiha

Wani dalili mai ƙarfi shine, yadda matasa da yawa ke tururuwa zuwa dandalin, domin samun magoya baya, wanda watakila hakan tasa hukumar ke ɗaukar ƙwaƙwƙwaran mataki domin ɗakile masu shigowa dandalin sababbi, daga aikata irin haka.

Ganduje Da Ƴan TikTok

Ɗaya daga cikin manya manyan abubuwa da suka ja hankali shine sa-toka-sa-katsin daya shiga tsakanin Mubarak Isa Muhammad da Nazifi Bala Muhammad, da kuma Gwabnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, rahoton Leadership.

Inda kotu ta kama su da laifi sakin wani faifan vidiyon dake ɓatawa gwamnan suna dashi da iyalin sa.

Bayan ɗaukar sati biyu a gidan ɗan kande, kotu ta basu horon share harabar kotu na sati biyu tare da yi musu bulala guda ashirin. Taɓdijam, domin kotun bata tsaya anan ba saida tace suyi faifan vidiyo su wallafa suna bawa gwamnan haƙuri, wanda hakan akayi.

Murja Kunya da Majalisar Malamai ta Jihar Kano

Murja Ibrahim Kunya tayi ƙaurin suna a TikTok. Itama ta shiga gidan gyaran hali na sati Uku bayan majalisar malamai ta shigar da ƙarar ta a kotun shari'ar Muslunci akan sakin video dake ɓatar da jama'a tare da barazana gare su, Legit ta rahoto.

Kara karanta wannan

Miyagun 'Yan Bindiga Sun Bude Wa Jami'an Tsaro Wuta, Da Yawa Sun Mutu a Kaduna

Murja da abokanta guda uku an cilla su gidan gyaran hali na satittika, tare da umartar, Ashiru Mai Wushirya, Aminu Ibrahim BBC da Sadik Sharif Umar da ita Murja Ibrahim Kunyar dasu share asibitin murtala har na sati Uku.

Rahoton Freedom Rediyo ya kara da cewa kotun ta umarci murja ta koma islamiyya dake ofishin hukumar harna tsawon wata shida sannan ta ɗaura bidiyon bada haƙuri. Kuma anyi hakan.

Mawaƙin TikTok da Hisbah

Bugu da ƙari, hukumar hisba ta kama wani mawaƙi waishi Al-Amin G-Fresh akan wasa da sallah a cikin bidiyon sa na TikTok, rahoton MI3 Novels.

Bayan wa'azi da tunatarwa, mawaƙin ya amsa laifin sa kuma ya tuba nan take.

Duk da dai ba'a hukunta shi ba, Hisba ta tauna tsakuwa don aya taji tsoro ta hanyar yi masa aikin malu, sannan tabashi shawarar ya koma islamiyya wanda ya yarda zai koma.

Kara karanta wannan

An Kashe Mutane 50, An Raunata Da Dama, An Kona Gidaje Yayin Hare-Hare A Binuwai

Umurnin Damke Ado Gwanja, Safarau Da Yan TikTok 8

A watan Agusta 2022, wata kotun shari'a ta umurci hukumar yan sanda ta damke wasu mutum 10 kuma ta bincikesu kan koyawa matasa rashin tarbiyya a kafafen ra'ayi da sada zumunta, wani jami'in kotun ya bayyanawa AFP.

Kotun ta bada umurnin ne tun ranar Talatar makon lauyoyi sun shigar da kara inda suka bukaci hukunta Ado Gwanja da ire-irensa bisa wakokin rashin tarbiyya da daurawa a yanar gizo, jami'in kotun Baba-Jibo Ibrahim ya bayyana hakan, Legit ta ruwaito.

Gargadin hukuma NCC game da TikTok

A watan Disamba 2022, Hukumar Sadarwa ta Najeriya ta gargadi 'yan Najeriya kan hadarin shiga sabuwar gasar Tik-Tok mai suna "Invisible Challenge" tana mai cewa hakan kan iya sawa wayoyinka bairos, rahoton Premium Times.

Tace wannan gasar na baiwa wasu damar shigar da bairos din cikin na'o'urorin da kuke amfani da ita, inda su ringa sa ma bairso din daga kwamfuwutar su inji NCC.

Kara karanta wannan

Zaben Shugaban Kasa, Majalisar Tarayya: Yan Sanda Sun Kama Fiye Da Mutum 203 Kan Laifukan Zabe

Wani Soja Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ya Shiga Hannun Hukuma

A wani labarin daban, Wani soja mai safarar miyagun ƙwayoyi a jihar Legas ya gurfana a gaban kotu domin girbar abinda ya shuka.

Lauyan hukumar NDLEA yace wanda ake ƙarar ya dade yana aikata wannan baƙar sana'a ta safarar miyagun ƙwayoyi.

Sai dai, wanda ake zargin ya musanta dukkanin laifukan da ake tuhumar sa da su a gaban kotun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel