Matsala Ta Kunno Daga Ƴan Kasuwa Duk da Bankuna Sun Fara Ba Da Tsohon Naira

Matsala Ta Kunno Daga Ƴan Kasuwa Duk da Bankuna Sun Fara Ba Da Tsohon Naira

  • Yayin da ake murna bankuna sun fara biyan kuɗi da tsoffin naira, yan kasuwa sun ce sam ba zasu karɓa ba a Legas
  • Da yawan su sun kafa sharadin cewa ba zasu karbi tsohon N500 da N1000 har sai sun ji daga bakin Buhari ko CBN
  • Kakakin CBN ya ce babu dalilin da zai sa ƴan kasuwa su ƙi amsar kuɗin tun da Kotu ta tsawaita wa'adinsu

Lagos - Wasu 'yan kasuwa da masu Tireda a jihar Legas sun ce zasu karbi tsohon N500 da N1000 ne kaɗai idan shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya fito ya ba da umarni, kamar yadda Punch ta ruwaito.

'Yan kasuwan sun shaida wa hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) a hira daban-daban cewa suna taka-tsantsan kuma suna dakon Buhari ko gwamnan CBN ya yi jawabi kan batun.

Kara karanta wannan

Shirin zabe: Ana shirin zabe, gwamnonin APC sun shiga zaman kus-kus da shugaban jam'iyya

Tsoffin kuɗi.
Yan kasuwa sun daina amfar tsohon kuɗi a Legas Hoto: thenation
Asali: UGC

Sun ce lokacin da Kotun koli ta ɗiba zai baiwa CBN damar buga sabbin takardun kuɗin kana ya rabawa bankuna domin su isa hannun al'umma, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Muna jiran Buhari ko CBN ya ba da umarni - Yan kasuwa

Mista Barnabas Israel, mai sayar da kayan abinci a Ori-Oke, ya nuna tantamar cewa da wuya idan akwai tsaffin kuɗin a bankuna kawo yanzu kuma tuni mutane suka maida na hannunsu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa ya ce:

"Any akwai tsoffin naira kuwa a gari domin mutane sun maida na hannun su. Kawo yanzu ba wanda ya zo shagona da tsohon kuɗi, idan ma wani ya kawo ba zan karɓa ba saboda babu mai amsa a yankinmu."

Misis Paulina Akuneme, wata mai sana'ar sayar da Burodi a Ili-ewe, Ikotun-Egbe, ta bayyana ra'ayinta kan batun da cewa:

Kara karanta wannan

"Ba Mu Ji Dadi Ba": Kwankwaso Ya Fusata, Ya Yi Allah Wadai Da Belin Ado Doguwa

"Bana son ganin tsohon kuɗi bayan wahalar da sha a baya wajen maida su banki lokacin da mahukunta suka ce sun zama mara amfani."
"Abinda na yi tsammanin Kotun zata yi shi ne ta umarci CBN ya buga sabbin kuɗin da zasu wadata a hannun'yan Najeriya. Mutane sun wuce wurin, ina da tabbacin zuwa Disamba wahala zamu kara fuskanta."

Wani mai sana'ar sayar da Doya, Alhaji Musa Jamiu, ya ce ba zai karɓi tsohon kuɗi ba har sai shugaban kasa ya umarci a ci gaba da karɓa.

"Shin Kotun koli ce ta mallaki CBN ko buga kuɗin? Wannan aikin CBN ne da gwamnatin tarayya su buga kuɗi kuma su baiwa mutane. Ba ruwana da hukuncin Kotu har sai sun amince."

"Kun san cewa N200 na yawo sakamakon umarnin FG da CBN, don haka aka dawo da ita mutane suka ci gaba da hada-hada," inji shi.

A wani labarin kuma Bankuna da dama sun fara baiwa kwastominsu tsoffin N500 da N100 bayan hukuncin Kotu

Kara karanta wannan

Shin Kwankwaso Ya Taya Zababben Shugaban Kasa Bola Tinubu Murna, NNPP Ta Yi Karin Haske

Wani ma'aikacin banki a Legas ya ce sun samu umarni daga CBN cewa kuɗin zasu ci gaba da zama halas har watan Disamba.

Yayin da aka tuntubi mai magana da yawun CBN, Isa Abdulmumin, ya ce bankuna na da ikon baiwa mutanr tsohon naira.

Asali: Legit.ng

Online view pixel