Bayan kwalliya, karanta anfanin lalle 9 ga ya mace

Bayan kwalliya, karanta anfanin lalle 9 ga ya mace

- Lalle na cikin wani sinadarin da ke dauke da alfanu iri iri, kuma addini ta kwadaitar da muyi lalle akwai sirrika acikin sa.

- Menene Amfanin Lallai?

Legit.ng ta kula in nace lalle wasu zasu dauka zanen henna nake nufi ko, to lalle dai na gargajiya wanda muka rabu da yinsa yanzu shi nake magana akai.

1) Na farko dai lalle Kariya ce daga sihiri, Kariya ce daga aljanu sannan kuma Kariya ce daga cututtuka da dama.

2) Yin lalle a kafa na zuqe cutar dake kafa sannan yana maintaining dumin mace, bi ma ana

yana inganta ni’imar mace ba tare da ya gushe ba.

3) Ga duk mace mai infection, ta tafasa lalle in ya dan huce sai ta yi sit bath dashi na sati biyu

in Allah ya yarda zata warke.

4) Ana iya sha ruwan lalle cokali 1 don wankin dattin ciki amma banda masu ciki.

5) Don gyaran Fata; lalle dai ba karamin tasiri yake dashi wajen gyara fata ba, domin shi

natural toner ne wanda ba bilicin yake yi ba amma yanasa haske mai kyau kuma yana goge dattin fata.

Bayan kwalliya, karanta anfanin lalle 9 ga ya mace
Bayan kwalliya, karanta anfanin lalle 9 ga ya mace

KU KARANTA: Jam'iyyar PDP ta tafka babbar asara a wannan jihar

6) A bangaren gyaran fuska, tana sa fuska tai kyalli, laushi, da haske in an kwaba da ruwan Kwai amma banda kwaiduwar kwan.ki kwaba ruwa ruwa amma ba sosai ba ki lizimci shafa shi kullum 30 mins kafin wanka sai Kinga bambanci a cikin sati biyu Insha Allahu.

7) Ga masu son hasken fata, ki kwaba lalle da ruwa, ki shafe a jikinki inya bushe ki dirje da man

zaitun za kiga canji.

8) Ga masu fama da pimples, yar’ uwa ki hada lemon tsami da lalle kwabi mai dan tauri amma ba sosai ba kina shafa wa a fuskar ki bayan watanni kuraje zasu mutu sannan tabo bazai zauna ba ga hasken fuska da laushi.

9) sannan gamai son kamshin fata, Ki kwaba lalle da turaren ki mai kyau na ruwa wanda ake durawa ki zuba isasshen ruwa a bucket ki sa garin lalle ta jika tai já zir sai ki tsiyaye ruwan ki diga turaren ki mai kamshi ciki Bayan kinyi wankan sabulunki sai ki dauraye jikinki dashi inkin lizimci haka to bake ba rabo da kamshin jiki in sha Allahu.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel