An Kama Dan Sanda Da Ya Bindige Dattijuwa Yar Shekara 80 Har Lahira A Adamawa

An Kama Dan Sanda Da Ya Bindige Dattijuwa Yar Shekara 80 Har Lahira A Adamawa

  • Wani jami'in yan sanda a jihar Adamawa ya harbe wata dattijuwa har lahira
  • Hukumar yan sandan jihar Adamawa ta janjanta tare da mika ta'aziyya ga iyalan marigayiyar
  • Kwamishinan yan sandan Jihar ya tabbatar da kama jami'in, tare da bada tabbacin dole doka tayi aiki a kansa

Adamawa - Rundunar yan sandan Jihar Adamawa ta kama wani jami'in ta bisa zargin kisa, Saja Aliyu Yusuf, dalilin mutuwar wata dattijuwa mai shekaru 80, mai suna Maryam Yerbure Abdullahi.

Marigayiyar an harbe ta kuma ta mutu a ranar Alhamis 16 ga watan Fabrairu, a Yola, babban birnin jihar, The Punch ta rahoto.

CP na Adamawa
An Kama Dan Sanda Da Ya Bindige Dattijuwa Yar Shekara 80 Har Lahira A Adamawa. Hoto: The Punch.
Asali: Facebook

An kuma binne ta ranar Juma'a biyo bayan faruwar al'amarin mai ban matukar kaduwa, kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Matashi Dan Shekara 20 Ya Yi Garkuwa Da Mahaifiyarsa A Zamfara, Ya Karbi Miliyan 30 Kudin Fansa

Yadda lamarin ya faru

An ruwaito cewa jami'in dan sandan ya harbi marigayiyar lokacin da ake kokarin kama wani matashi a Doubelli, wani bangaren Jimeta - Yola, daren Alhamis da misalin 9:45 na dare.

Yusuf, wanda ya fita aikin sintiri tare da wasu ma'aikatan ofishin yan sanda na Doubelli, ya biyo wani matashi da ya ke tunanin dan uwan matar ne a daidai lokacin da zai shiga gidan su amma wasu mazauna gidan suka bukaci jin dalilin kama shi.

Ana tsaka da cacar baki, sai Saja Yusuf ya ja kunamar bindigarsa don tarwatsa taron da ke wajen amma sai ya sake ta akan dattijuwar da kuma wani da abin ya shafa, da aka bayyana sunan sa Arfad, wanda ya samu rauni daga harsashin a kirjin sa.

Kwamishinan yan sandan jihar, CP Afolabi Babatola, da ya ke jajen mutuwar Maryam a ranar Juma'a ya sanar da kama jami'in da ya yi kisan.

Kara karanta wannan

Yan Ta'adda Sun Kai Hari Sansanin Horaswa Ta Hukumar INEC

Hakan na kunshe ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje ya fitar, mai taken ''kwamishinan yan sanda ya janjanta mutuwar Maryam Abdullahi, an kama Saja Aliyu Yusuf.''

Mai magana da yawun yan sandan, yayin da yake mika ta'aziyya ga iyalan marigayiyar, ya tabbatar da cewa kwamishinan ya umarci mataimakin kwamishina da ke kula da sashen binciken manyan laifuka CID da su cigaba da gudanar da bincike tare da tabbatar da doka tayi aikinta.

A baya kun ji cewa an kama wasu sojoji biyu a jihar Yobe kan zargin kashe malamin addinin musulunci, Sheikh Goni Aisami da aka kashe a hanyar Gashuwa zuwa Kano.

Majiyoyi sun rahoto cewa wadanda ake zargin sun halaka malamin ne bayan ya dauke su a motarsa don rage musu hanya daga Nguru zuwa Jaji-maji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel