Mutanen Kaduna Sun Yi Watsi Da Umurnin El-Rufai, Suna Ta Rububin Kai Tsaffin Kudadensu CBN

Mutanen Kaduna Sun Yi Watsi Da Umurnin El-Rufai, Suna Ta Rububin Kai Tsaffin Kudadensu CBN

  • Wasu mazauna Kaduna sun ki sauraron umurnin Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna na cewa su cigaba da amfani da tsaffin kudadensu
  • El-Rufai cikin jawabin da ya yi a ranar Alhamis ya ce kotun koli ba ta riga ta haramta amfani da tsaffin kudaden ba don haka kowa ya cigaba da kashe wa
  • Sai dai duk da hakan, rahotanni sun nuna cewa daruruwan mazauna Kaduna sun cigaba da tururuwa zuwa babban bankin kasa, CBN, na Kaduna don mayar da tsaffin kudaden

Kaduna - Duk da matakin da Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya dauka na halasta kashe tsaffin kudi a jiharsa, wasu mazauna jihar suna ta zuwa babban bankin kasa, CBN, don kai tsaffin kudinsu.

A wata jawabi da ya yi a safiyar ranar Alhamis, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce tsohon naira 200 ne kadai ya halasta a kashe, ya umurci yan Najeriya su mayar da tsaffin N500 da N100 zuwa ofisoshin CBN.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: El-Rufai Ya Bijire Wa Umurnin Buhari, Ya Ce A Cigaba Da Kashe Tsohon Kudi A Kaduna

El-Rufai
Mutanen Kaduna Sun Yi Watsi Da Umurnin El-Rufai, Sun Kai Tsaffin Kudadensu CBN. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Amma, El-Rufai ya bukaci mazauna jiharsa su cigaba amfani da tsaffi da sabbin nairan ba tare da fargaba ko tsoro ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnan, kuma ya ce zai rufe duk wani kanti ko wurin kasuwanci da ya ki karbar tsohon takardun nairan ya kuma hukunta masu wurin.

Wakilin Daily Trust ya rahoto cewa tun misalin karfe 3 na dare, mutane sun rika zuwa harabar babban bankin na kasa don tsoron yin asarar kudinsu.

Wasu mazauna Kaduna sun magantu kan batun mayar da tsaffin kudinsu CBN

Kuma, misalin karfe 7.30 na safiya, an ga daruruwan mutane suna jiran a fara karbar kudaden.

Badamasi Aliyu, wani mazaunin Kaduna wanda ya yi magana da wakilin Daily Trust ya ce:

"A Kawo na ke zaune, karamar hukumar Kaduna ta Arewa amma ina bukatar zuwa ofishin CBN da wuri. Dole na kama otel da ke kusa saboda kada inyi latti. Na taho nan misalin karfe 3 na dare, ni ne mutum na 134. Abin da wahala amma ina addu'ar samun damar mayar da kudin nawa."

Kara karanta wannan

Yanzu: Ku mayar da N1000 da N500 ofishin CBN, zamu fito da tsaffin N200 a cigaba da amfani, Buhari

Wata mazauniyar Kaduna, Mary Auta, ta ce ta kai kudinta bankin ranar Alhamis amma ba ta yi nasarar mayar da kudin ba don mutane sunyi yawa.

Ta ce:

"Na zo nan ranar Alhamis, ba kowa, ba ma'aikatan banki da za su karbi kudin mu. Ina fatan yau (Juma'a) za su karbi kudin."

Jami'in CBN ya yi martani

Mukhtar Maigamo, wani ma'aikacin CBN ya ce an fara karbar tsaffin kudin kuma suna karbar kudin daya bayan daya.

A cewarsa:

"Mutane da dama sun taho da kudi kasa da N500,000 kuma mu daga N500,000 zuwa sama muke karba. Wadanda kudinsu bai kai N500,000 ba su tafi bankunan kasuwanci."

An tafka dirama yayin da wani ya tafi CBN mayar da N50m a buhuna a Kano

A bangare guda, kun ji cewa wani mutum ya dauki hankulan mutane bayan bidiyon yadda ya tafi banki mayar da tsaffin kudade har naira miliyan 50 cikin buhuna a Kano ya bazu.

Kara karanta wannan

Canjin Kudi: Gwamnati Tana Rokon a Sasanta, Amma Mun Ki Yarda Inji El-Rufai

Asali: Legit.ng

Online view pixel