Mazauna Kaduna Sun Roki 'Yan Ta'adda Su Bari A Yi Zabe A Garuruwansu

Mazauna Kaduna Sun Roki 'Yan Ta'adda Su Bari A Yi Zabe A Garuruwansu

  • Al'umma a garin Birnin-Gwari na cikin fargabar yadda zabe zai gudana duba da matsalar tsaro a yankin
  • Kungiyar BEPU ta ce tana tattaunawa da kungiyoyin yan ta'adda daban daban don ganin an gudanar da zabe cikin lumana a yankin
  • Kungiyar ta kuma yabawa hukumar zabe bisa sauya wasu akwatunan zabe zuwa sansanin yan gudun hijira biyo bayan raba su da muhallinsu

Kaduna - Karatowar babban zaben 2023, al'ummar da hare-haren yan ta'adda ke addaba a Birnin-Gwari da ke karamar hukumar Birnin-Gwari ta Jihar Kaduna sun ce sun fara tuntubar kungiyoyin yan ta'adda daban-daban don ganin an gudanar da zabe cikin lumana a yankin, rahoton Punch.

Shugaban kungiyar masu son ganin cigaban masarautar Birnin-Gwari (BEPU), Ishaq Kasai, a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, ya ce hakan ya zama dole in aka yi la'akari da irin matsalar tsaron da su ke ciki inda yan bindiga suka kori kusan garuruwa 100 tare da raba sama da mutum 50,000 da muhallinsu da yan ta'adda suka yi a karamar hukumar.

Kara karanta wannan

Yan Ta'adda Sun Kai Hari Sansanin Horaswa Ta Hukumar INEC

Kaduna Town
Mazauna Kaduna Sun Roki 'Yan Ta'adda Su Bari A Yi Zabe A Garuruwansu. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Dole mu yi sulhu da yan ta'adda idan muna son a yi zabe - Shugaban BEPU

Sanarwar na dauke da taken, 'Zaben 2023: zama da kungiyoyin yan ta'adda ne zai bada dama a gudanar da zabe cikin lumana a Birnin-Gwari'.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sa, zantawar su da kungiyoyin ta'addanci daban daban don yin sulhu zai bada damar a gudanar da zabe a mazabu 10 cikin 11 da ke karamar hukumar don sauke nauyin zabar shugabannin su a zaben da zai gudana sati mai zuwa.

Shugaban na BEPU ya shaida cewa idan ba sulhu aka yi da yan ta'adda ba al'umma ba za su iya fitowa su kada kuri'a a babban zabe mai zuwa ba a karamar hukumar da hare haren ta'addanci ya tagayyara.

Kasai ya jinjinawa INEC saboda samar da rumfunan zabe a wuraren da ake bukata

Kara karanta wannan

Karancin Kudi: Gwamna Ya Samar Da Bas Din Kyauta Don Ragewa Al'ummarsa Radadin Halin Da Ake Ciki

Kasai ya kuma yabawa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC saboda sauya wasu akwatuna daga wuraren da aka kori al'umma zuwa wuraren da suke zaune a matsayin yan gudun hijira.

Ya ce:

''Yayin da zaben 2023 ke kara matsowa, babbar damuwar mu shine mutanen mu, hadda wanda aka raba da muhallinsu, don a ba su dama su sauke nauyin su a wuraren da aka kebe su ta hanyar ba su dama su zabi wanda ransu ya ke so ba tare da tsoro ko fargaba ba.
''A wannan gabar, muna so mu yabawa kokarin hukumar zabe mai zaman kanta na sauya wasu akwatunan zabe daga inda aka kori al'umma zuwa inda suke killace a matsayin yan gudun hijira. Babu shakka hakan zai ba su wajen sauke hakkin su na kada kuri'a.
''Abu na biyu shine yadda kayan zabe da ma'aikata za su isa wuraren zaben a karamar hukumar ranar zabe, musamman yankunan da ke da matsalar tsaro sosai, kamar Gabashi da Kudancin karamar hukumar.

Kara karanta wannan

CBN: Tinubu Ya Gabatar Da Babban Bukata 1 Bayan An Yi Zanga-Zanga Kan Karancin Naira a Fadin Najeriya

''Mazabu 11 ne a Birnin-Gwari kuma 10 a ciki na fama da matsalar tsaro da idan ba abi matakan da ya dace ba za a samu tsaiko a gudanar da zabe.''

Ya kara da cewa:

''Duk da dai, mun san irin shirin da akayi don shawo kan matsalar, musamman yadda aka yi kokarin tattaunawa da kungiyoyin yan ta'adda a wuraren da abin yafi kamari don samun damar gudanar da zabe cikin lumana a yankunan.
''Ko a lokacin aikin hukumar kidaya na tantance unguwanni da gidaje irin haka aka yi aka samu nasarar aikin, da izinin yan bindigar, ma'aikatan kidaya sun shiga tare da tantance ko ina.
''Saboda haka, mun lura cewa, duba da abin da muka gani, sulhu da yan ta'adda ne kadai hanya don su bada dama a gudanar da zaben 2023 lafiya a mazaba kusan 10 da akwati sama da 100 a karamar hukumar Birnin-Gwari.
''A halin yanzu, saboda rashin tsaro, INEC ta soke akwati guda a mazabar Gayam da ke karamar hukumar. Wannan mazabar na daya daga cikin 240 da INEC ta soke a fadin kasa saboda matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

Daina Karbar Tsoffin Naira Ya Birkita Najeriya, An Barke Da Zanga-Zanga a Kwara Da Wasu Jihohi 2

''Saboda haka mu ke shawartar hukumomi da su zauna da masu ruwa da tsaki, musamman shugabancin unguwanni duk a shirin yin zaben 2023 lafiya a karamar hukumar Birnin-Gwari.''

Ortom ya ce ba zai zuba ido yana kallon yan ta'adda na kashe mutanen jiharsa ba

A wani rahoton, gwamnan jiar Benue, Samuel Ortom ya ce gwamnatinsa ba za ta nade hannu tana kallon yan ta'adda na halaka mutanen jiharsa ba.

Gwamnan ya furta hakan ne yayin bikin raba motocci na aiki ga jami'an kungiyar sa kai ta (BSCVG) na jihar da gwamnatinsa ta kirkira.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164