Yan Ta'adda Sun Kai Hari Sansanin Horaswa Ta Hukumar INEC

Yan Ta'adda Sun Kai Hari Sansanin Horaswa Ta Hukumar INEC

  • Wasu gungun yan bindinga sun kai hari wata makaranta da ke a mazaunin sansanin horar da ma'aikatan INEC a Anambra
  • Yan bindigar sun Kai harin makarantar Ukpor High School da ke karamar hukumar Nnewi South, sai dai babu wanda ya rasa rai ko ya illata a harin
  • Shaidun gani da ido sun ce zai wahala ma'aikatan su samu kwarin gwiwar yin aiki cikin sati guda yayin da yan sanda ke bada tabbacin ingantaccen tsaro a yankin

Anambra - Yan bindiga ranar Alhamis sun kai hari makarantar Ukpor High School, daya daga cikin sansanin horas da ma'aikatan hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a karamar hukumar Nnewi South, Jihar Anambra.

Yan bindigar sun kawo tsaiko ga horon a shirin babban zabe mai zuwa, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Karancin Kudi: Gwamna Ya Samar Da Bas Din Kyauta Don Ragewa Al'ummarsa Radadin Halin Da Ake Ciki

Taswirar Anambra
Yan Bindiga Sun Kai Hari Sansanin Horaswa Ta Hukumar INEC. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Wata majiya daga yankin ta ce lamarin da ya faru da misalin 5:35 na yamma, ya bar dalibai, yan bautar kasa da sauran masu daukar hoto cikin zullumi.

Majiyar ta ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

''Ina tantamar yadda mutanen nan za su yadda su yi aiki wa INEC a yankin biyo bayan abin da ya faru. Amma mun gode Allah babu wanda aka kashe a harin. Lamarin ya bani tsoro sosai. Ba mu da tabbacin mutanen za su bari muyi aiki a sati mai zuwa."

Mai magana da yawun rundunar yan sandan Jihar Anambra, DSP Tochkuwu Ikenga, wanda ya tabbatar da faruwar al'amarin, ya bayyana yadda jami'an tsaro suka dakatar da maharan daga sace ko illata masu dauka da bada horon ba.

Ya ce:

''Biyo bayan matakan tsaro da kwamishinan yan sanda, CP Echeng Echeng, wanda ke da iganci da karfin murkushe duk wani ba zata musamman da zai kawo tsaiko a harkar zabe a jihar, hadin gwiwar tawagar jami'an tsaro a yau 16/2/2023 da misalin 5:35 na yamma sun samu nasarar cetowa tare da hana yan bindiga cutar da ma'aikatan hukumar zabe da ke aikin horarwa a Ukpor High School, karamar hukumar Nnewi South.

Kara karanta wannan

Kazamin Rikici Ya Barke Tsakanin Yan Sanda Da Matasa A Bauchi, Da Dama Sun Jikkata

''Ma'aikatan hukumar INEC, da yan bautar kasa, daliban jami'a da wasu jami'an MDA da ke sansanin daukar horon aikin zabe sun samu tsaiko daga yan bindiga. Amma ba a rasa rai ba.
''An kara tsaurara matakan tsaro a yankin kuma ana cigaba da bibiya don kama masu laifin. Za mu cigaba da sanar da halin da ake ciki akan lamarin.''

An kacame tsakanin matasa da yan sanda a jihar Bauchi

A baya kun ji cewa wani rikici ya barke tsakanin matasan Bauchi da jami'an yan sandan birnin tarayya Abuja da a garin Magama-Gumau na karamar hukumar Toro.

Rahotanni sun ce yan sandan sun yi dirar mikiya a garin ne domin gudanar da wani aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel