El-Rufai Ya Umurci Ma'aikatun Gwamnatin Kaduna Su Ci Gaba Da Karbar Tsoffin Kudi

El-Rufai Ya Umurci Ma'aikatun Gwamnatin Kaduna Su Ci Gaba Da Karbar Tsoffin Kudi

  • Gwamna Nasir El-Rufai ya bukaci ma'aikatun gwamnatin Kaduna da su ci gaba da karbar tsoffin N500 da N1000
  • Gwamnatin jihar Kaduna ta ce wannan umurni nata ya yi daidai da wanda kotun kolin Najeriya ta bayar kan takardun naira
  • El-Rufai ya yi umurcin cewa duk wanda ya kawo tsoho ko sabon kudi toh lallai hukumomin gwamnatin su karba

Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin Nasir El-Rufai ta umurci ma'aikatu da hukomin gwamnatin jihar da su ci gaba da karbar tsoffin kudi.

A wata sanarwa da mai ba gwamnan shawara ta musamman kan kafofin watsa labartai, Muyiwa Adekeye ya saki a ranar Lahadi, 19 ga watan Fabrairy, ya ce a ci gaba da hada-hada da tsoffi da sabbin kudi a jihar.

Nasir El-Rufai
El-Rufai Ya Umurci Ma'aikatun Gwamnatin Kaduna Su Ci Gaba Da Karbar Tsoffin Kudi Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Hukuncin umurnin wucin gadi na kotun koli ne

Kara karanta wannan

Karin Bayani: An Kirkiri Sauyin Naira Ne Don Durkusar Da Kasuwancin Kano, In Ji Kwamishina

Gwamnatin jihar ta ce umurnin na daidai da hukuncin wucin gadi na kotun koli kan takardun naira.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Daidai da umurnin wucin gadi na kotun koli, gwamnatin jihar Kaduna ta umurci ma'aikatunta, da hukumomin gwamnati su tabbatar da cewa sun ci gaba da karbar tsoffi da sabbin kudade yayin biyan kudi.
"Dokar jihar Kaduna bata yarda da barin wani jami'i na hukumomin gwamnati ya karbi tsabar kudi na haraji ba.
"Jami'an karbar haraji da hukumomin gwamnatin jihar suka amincewa karbar kudin suna baiwa jama'a tsarin biyan tsabar kudi, kuma ana sanya ran za su ba umurnin kotu hadin kai.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari dai ya ayyana cewa tsoffin N500 da N1000 ba halastattu bane amma El-Rufai ya bijire, cewa za a ci gaba da amfani da su a Kaduna har sai idan kotun koli ta hana.

Kara karanta wannan

Naira: Shugaba Buhari Na Yiwa Kotun Koli Karan-Tsaye, Bai Dace Ba: Kakakin Majalisa

Gwamnan na Kaduna yana cikin gwamnonin Arewa uku da suka shigar da gwamnatin tarayya da babban bankin Najeriya (CBN) a kotun koli.

Na sha mamakin ganin gwamnonin APC na caccakar Buhari, Kwankwaso

A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso ya ce ya ji mamaki ganin cewa lamarin kudi ya kai matakin da har wasu na zagin shugabanni.

Kwankwaso ya ce watakila akwai kamshin gaskiya a ikirarin hukumar EFCC na cewa wasu gwamnoni sun boye kudade a gidajensu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel