Yan Bindiga Da Dama Sun Sheka Barzahu Yayin Musayar Wuta da Yan Sanda a Anambra

Yan Bindiga Da Dama Sun Sheka Barzahu Yayin Musayar Wuta da Yan Sanda a Anambra

  • sDakarun yan sanda a jihar Anambra sun yi nasarar dakile harin yan bindiga a caji Ofis ɗin da ke Nkwelle-Ezunaka
  • Mai magana da yawun hukumar, Tochukwu Ikenga, ya ce dukkan yan bindiga 5 da suka kai harin an kashe su
  • A cewarsa yanzu haka dakaru sun matsa ƙaimi a yankin kuma ana ci gaba da gudanar da bincike

Anambra - Miyagun 'yan bindiga 5 da kuma ɗan sanda guda ɗaya sun rasa rayuwarsu yayin wani artabu a Caji Ofis ɗin Nkwelle Ezunaka, ƙaramar hukumar Oyi, jihar Anambra da safiyar Lahadin nan.

Wannan sabon harin na zuwa ne awanni 24 bayan kai hare-hare biyu a Ukpo da Ogidi, inda 'yan sanda uku suka mutu kuma wasu Sojoji suka samu raunuka.

Taswirar jihar Anambra.
Taswirar jihar Anambra Inda Yan Bindiga Da Dama Sun Sheka Barzahu Hoto: Anambra State
Asali: Depositphotos

Wani mazaunin yankin ya ce maharan sun je da yawa da misalin karfe 3:30 na dare wayewar garin yau Lahadi kuma suna sanye da baƙaƙen tufafi, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Talaka Na Shan Wuya, Duk Da Ina Gwamna Sababbin Kuɗin Sun Yi Min Wuyar Samu -Gwamna Ya Koka

"Yan bindigan sun iso Caji Ogis din bayan musayar wuta da yan sanda. Mun ji ƙarar harbe-harbe mai tsanani kuma mun ga Mota a Caji ofis ɗin tana ci da wuta. Artabu da maharan ya yi ajalin ɗan sanda ɗaya."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ɓiyu daga cikin 'yan bindigan sun sheƙa barzahu kuma ana tsammanin ɗayansu ya ji raunuka masu girma," inji mutumin.

Da yake tabbatar da lamarin, jami'in hulɗa da jama'a na hukumar yan sandan Anambra, Tochukwu Ikenga, ya ce 'yan ta'adda biyar da jami'i ɗaya ne suka mutu a musayar wutan.

Ya ƙara da cewa lamarin ya shafi ɗaya daga cikin Ofisoshin wurin kuma maharan sun ƙona Motar Sintirin da suka taras a gaban Caji Ofis ɗin.

Kakakin yan sandan ya ce:

"Jami'an tsaro da suka ƙunshi yan sanda da Sojoji a yau 19 ga wata da karfe 5:58 na safe sun sheƙe tawagar yan bindiga biyar, sun kwato AK-47, motar Sienna, layu da sauransu."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Zanga-Zanga Ta Sake Ɓarkewa Kan Karancin Kuɗi, An Cinnawa Bankuna Wuta

"Hakan ta faru ne yayin da Dakarun suka kai ɗauki kan kiran gaggawa daga Hedkwatar yan sanda 3 3 da ke Nkwelle-Ezunaka, Oyi LGA. Maharan su 5 ɗauke da bindigu, bama-bamai da bam ɗin Fetur sun yi kokarin kutsa kai Ofishin."
"Amma jajirtattun yan sanda suka tarbe su aka yi musayar wuta, bisa rashin sa'a ɗan sanda ɗaya ya ji munanan raunuka, ofishi ɗaya ya ƙone sanadin Bam ɗin da maharan suka jefa."

Bugu da ƙari, mai magana da yawun yan sandan ya ce a halin yanzun komai ya koma yadda yake kuma jami'an tsaro sun ƙara tsananta sintiri a yankin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Yan bindiga sun kai hari wurin taron APC

A wani labarin kuma Mutum Daya Ya Mutu Yayin da Yan Bindiga Suka Kai Harin Wurin Kamfe a Jihar Ebonyi

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun bude wa mahalarta taron kamfen wuta jin kaɗan bayan kammala wa suna shirin tafiya gida.

Kara karanta wannan

Ana Dab da Zaɓen 2023, Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Wurin Kamfe, Sun Buɗe Wuta

An tattari cewa baya ga mutum ɗaya da suka yi ajalinsa, maharan sun lalata motoci biyu yayin harin na jiya Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel