Mutum Daya Ya Mutu Yayin da Yan Bindiga Suka Kai Harin Wurin Kamfe a Ebonyi

Mutum Daya Ya Mutu Yayin da Yan Bindiga Suka Kai Harin Wurin Kamfe a Ebonyi

  • Yan bindiga sun halaka mutum ɗaya yayin da suka kai harin ta'addanci wurin kamfen jam'iyyar APC a jihar Ebonyi
  • Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a yankin ƙaramar hukumar Isielu yayin kamfen ɗan takarar Sanata
  • Maharan sun lalata motoci yayin harin wanda suka bude wa magoya baya wuta kan mai uwa da wabi

Ebonyi - Wasu miyagun 'yan bindiga sun kashe mutum ɗaya a wurin taron kamfen All Progressive Congress (APC) a jihar Ebonyi, kudu maso gabashin Najeriya.

Rahoton The Nation ya nuna cewa wata matar ɗan jarida a jihar ta shallake rijiya da baya lokacin harin domin 'yan bindigan buɗe masu wuta suka yi.

Lamarin ya faru ne a a gundumar Ezzagu da ke yankin ƙaramar hukumar Isielu lokacin da ɗan takarar Sanatana APC a mazaɓar Ebonyi ta tsskiya ya je kamfe garin.

Kara karanta wannan

2023: Abinda Tinubu Ya Yiwa Borno Lokacin Boko Haram da Babu Wanda Ya Taɓa Mana, Gwamna Zulum

Harin yan bindiga
Mutum Daya Ya Mutu Yayin da Yan Bindiga Suka Kai Harin Wurin Kamfe a Ebonyi Hoto: thenation
Asali: UGC

Wani haifaffen yankin, Mista Benjamin Nworie, wanda matarsa ta ga mutuwa muraran amma ta tsallake rijiya da baya ya bayyana yadda maharan suka shiga wurin, suka bude wa magoya baya wuta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce an gama taron yakin neman zaɓen lami lafiya amma lokacin da mahalarta taron ke shirin kama hanyar komawa garuruwansu, ba zato 'yan bingidan suka kunno kai kana suka buɗe masu wuta kan mai uwa da wabi.

A kalamansa ya ce:

"Da kusan misalin kare 5:30 na yammacin ranar Asabar, watan Fabrairu, na samu kiran gaggawa daga matata, Eunice, ta faɗa mun tana cikin haɗari. Duk hankalinta ya tashi ta kiɗime."
"Ta mun bayanin cewa tana cikin jeji ta buya bayan guduwa domin neman tsira, nan take na tura tawaga daga kauyen makota suka ceto ta, ba abinda ya same ta."

Kara karanta wannan

"Muhimman Abu 5" Abinda Atiku Ya Bayyana Wa Yan Najeriya a Wurin Kamfen PDP Na Karshe Gabanin Zabe

Nworie, mataimakin shugaban ƙungiyar 'yan jarida (NUJ) reshen Ebonyi, ya ce matarsa ta je wurin ne tare da shugaban Ogboji General Assembly, John Anyalagu, matarsa da ƙaninsa, Emeka Nwusulor.

"Bisa rashin sa'a, suna tsaye suna jiran John ya ɗauko mota daga ciki ya zo su dawo nan Abakaliki, ba zato maharan suka kutso suka kashe Emeka wanda ke tsaye."

A cewarsa bayan wannan kisan, maharan sun kaca-kaca tare da ƙona motar Hiace Bus da wata mota daban daga bisani suka yi gaba, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Yan bindiga sun harbi shugaban PDP a Imo

A wani labarin kuma kun ji cewa wasu mahara sun harbi shugaban PDP na matakin gunduma a jihar Imo

An tattaro cewa shugaban PDP a gudumar Ogbaku, ƙaramar hukumar Mbaitolu, ya shiga gida da daddare ba tare da sanin 'yan bindiga sun masa tsinke ba.

Wata majiya ta bayyana cewa tuni aka garzaya da shi Asibiti wanda har yanzu ba'a bayyana ba domin kula da lafiyarsa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An Bindige Ɗan Babban Jigon PDP Har Lahira, Bayanai Sun Fito

Asali: Legit.ng

Online view pixel