Duk Da Ina Matsayin Gwamna Sababbin Kuɗi Sun Yi Min Wuyar Samu

Duk Da Ina Matsayin Gwamna Sababbin Kuɗi Sun Yi Min Wuyar Samu

  • Gwamnan jihar Osun ya koka kan yadda duk da matsayin sa na gwamna amma sababbin kuɗi sun yi masa wahalar samu
  • Gwamna Ademola Adeleke ya bayyana cewa har yanzu sababbin kuɗin basu isa hannun sa ba
  • Gwamnan yayi kira ga babban bankin Najeriya (CBN) kan hukunta duk masu hannu kan ɓoye sababbin kuɗin

Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke, ƙarancin sababbin kuɗin da ake fama da shi na sanya mutane cikin baƙar wahala, inda yake cewa duk da matsayin sa na gwamna, baya da sababbin kuɗin.

Adeleke ya koka kan yadda ƙarancin kuɗin ya sanya mutanen jihar cikin tsaka mai wuya inda yace yana bakin ƙoƙarin sa wajen ganin an yayyafawa fitinar da ka iya ɓallewa ruwa a jihar. Rahoton Vanguard

Adeleke
Duk Da Ina Matsayin Gwamna Sababbin Kuɗi Sun Yi Min Wuyar Samu
Asali: Instagram

Yace zai tabbatar bankuna da ofishin babban bankin Najeriya (CBN) na jihar sun samu kariya.

Kara karanta wannan

Karancin Kuɗi: Marasa Lafiya Na Shan Wuya, Magani Yayi Musu Wahalar Samu, Kungiyar Likitoci

Da yake jawabi ga jami'an CBN ranar Litinin a ofishin sa, Adeleke ya nuna damuwar sa kan ƙarancin sababbin kuɗin, inda yayi kira ga CBN da hukunta duk bankunan da ke da hannu wajen azabtar da al'umma. Rahoton Daily Post

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Mutane ne suna da haƙuri amma bai kamata muyi wasa da haƙurin su ba. Shiyasa na kira wannan taron. Meyasa babu sababbin kuɗin? Shin babu sune ko ƙaranci suka yi?" A cewar gwamnan

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin sa a shirye take ta haɗa hannu da CBN domin musayar kuɗin, inda ya gayawa tawagar CBN ɗin cewa jihar na yin bakin ƙokarinta wajen ganin mutane sun kwantar da hankulan su.

“Kwata-kwata babu sababbin takardun kuɗi. Duk da ina matsayin gwamna, bani da sababbin kuɗin. Kaga mutanen mu kenan sai sun sha baƙar wahala kafin su samu sababbin kuɗin tunda ko gwamnan su ma baya da su."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Gamu da Gamonsu, An Kashe Su Baki Ɗaya Yayin da Sukai Yunkurin Kai Hari

"Bai kamata mu kai mutane maƙura ba game da haɗin kan da suke bamu. A matsayin mu na shugabanni nauyi ne a kanmu mu biya buƙatu da share hawayen mutanen mu"

Amarya Ta Fusata Bayan Gano Wata Cin Amana Da Ƙawarta Tayi Da Angonta

A wani labarin na daban kuma, wata amarya ta nuna ɓacin ranta bayan ta gano wani babban sirri da angonta da babbar ƙawarta suka ɓoye mata.

Tace atabau ta fasa auren.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng