Kotu Ta Yanke Sirikin Obasanjo Daurin Shekaru 7 A Gidan Yari

Kotu Ta Yanke Sirikin Obasanjo Daurin Shekaru 7 A Gidan Yari

  • Wata kotu na musamman a jihar Legas ta yanke wa surukin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Dr John Abebe, daurin shekaru 7 a gidan gyaran hali
  • An yanke wa Dr Abebe hukuncin ne bayan samunsa da laifin almundaha da kirkirar takardun karya a harkokin da ya yi da wata kamfanin man fetur
  • Sai dai kotun ta bawa Dr Abebe zabin biyan tara ta naira miliyan 50 wanda za a iya a cikin kwanaki 30 kacal don kauce wa zuwa gidan yarin

Jihar Legas - An yanke wa Dr John Abebe, suruki ga tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo hukuncin daurin shekaru bakwai saboda almundaha da 'kirkirar karya'.

Mai shari'a Mojisola Dada na kotun laifuka na musamman ta Ikeja ta bada hukuncin a ranar Asabar amma da zabin biyan tarar Naira miliyan 50 da za a biya cikin kwana 30, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Karya ne: Fadar Shugaban Kasa ta Karyata Zargin El-Rufai da Ganduje

Abebe
Kotu Ta Yanke Sirikin Obasanjo Daurin Shekaru 7 A Gidan Yari. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hukumar yaki da rashawa EFCC ta gurfanar da Abebe, wanda kani ne ga tsohuwar first lady, Stella Obasanjo a kotu kan zarginsa da 'kirkirar karya'.

A tuhumar, EFCC ta yi ikirarin cewa Abebe “da sane ya kirkiri” wata takarda ta ranar 30 ga Nuwamba, 1995 da BP Exploration Nigeria Limited ya rubuta zuwa ga Inducon Limited.

Alkalin ya yanke hukuncin ne bayan mai shigar da kara ya tabbatar da hujja kan zargin kuma aka yanke hukuncin da ya da ce.

A cewar EFCC, Dr Abebe kuma ya yi kokarin hana doka yin aikinta ta hanyar gabatar da wasikar bogi ta ranar 30 ga watan Nuwamban 1995 'a matsayin hujja' a kotu a kara mai lamba FHC/L/CS/224/2010 tsakanin Dr John Abebe da Inducon Nigeria Limited da Statoil Nigeria Limited.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Rikici Ya Barke A Jihar Legas Kan Lamarin Daina Karancin Naira

Hakazalika, kamfanin man fetur mai suna Statoil Nigeria Limited a ranar 22 ga watan Yunin shekarar 2010 ta kuma zargi Dr Abebe ta kirkirar takardar bogi, rahoton The Nation.

Statoil Nigeria Limited ta yi zargin cewa wanda aka yi karar ya kirkiri wasu sassan yarjejeniya na raba riba (Net Profit Interest Agreement (NPIA) mai dauke da kwanan wata na 30 ga watan Nuwamban 1995 da British Petroleum (BP) ya rubuta.

An yanke wa wani hukuncin dauri a gidan yari saboda satar doya

Wata kotu a Jihar Kwara ta yanke wa wani Abubakar Bani hukuncin daurin wata shida a gidan gyaran hali saboda samunsa da satar doya.

Nigerian Tribune ta rahoto cewa hukumar tsaro ta NSCDC ta jihar Kwara ne ta gurfanar da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel