Rikici Ya Barke A Jihar Legas Kan Lamarin Karancin Naira

Rikici Ya Barke A Jihar Legas Kan Lamarin Karancin Naira

  • An ji harbe-harben bindiga a kasuwar Mile 12 dake jihar Legas sakamakon kin karbar tsaffin takardun Naira
  • Direbobi, fasinjoji da sauran jama'a sun arce daga hanyar gudun kada rigimar ta ritsa da su
  • Kakakin hukumar yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya fitar da jawabi kan abinda ya haddada rigimar

Mazauna unguwar Mile 12 dake jihar Legas sun waye gari ranar Juma'a, 12 ga Febrairu, da jin harbe-harben bindiga yayinda wasu matasa suka tayar da tarzoma.

Wannan abu na faruwa ana saura kwanaki 8 da zaben shugaban kasa.

Wasu masu idon shaida sun bayyana abinda suka gani kuma sun daura bidiyoyi a kafar Tuwita.

Sanwo
Rikici Ya Barke A Jihar Legas Kan Lamarin Karancin Naira
Asali: Original

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya fitar da jawabi inda ya bayyana cewa an fara rigima ne saboda yan kasuwar Mile12 sun ki karbar tsaffin takardun Naira.

Kara karanta wannan

Karancin Kudi: Gwamna Ya Samar Da Bas Din Kyauta Don Ragewa Al'ummarsa Radadin Halin Da Ake Ciki

Yace yanzu an kwantar da tarzomar.

A cewarsa:

"Koma ya dawo daidai yanzu kuma motoci da mutane na iya wucewarsu. Jami'anmu na wajen don tabbatar da doka da oda."

Rigimar ta fara yaduwa sauran unguwannin Legas

Rikicin ya yadu unguwannin Agege, Ikorodu, Ketu, Ojota da Iyana-Iba, rahoton PMNews.

Kakakin yan sandan wanda ya sake tabbatar da hakan yace:

"Da gaske ne. Mun tura jami'ai wajen. Ku bi a hankali muna kula da lamarin."

Asali: Legit.ng

Online view pixel