Shugaba Buhari ya kara wa’adin amfani da tsaffin Naira da kwanaki 60 kuma a dawo da tsaffin kudi

Shugaba Buhari ya kara wa’adin amfani da tsaffin Naira da kwanaki 60 kuma a dawo da tsaffin kudi

  • Kamar yadda akayi alkawari, Shugaba Buhari ya gabatar da jawabi ga yan Najeriya kan Naira
  • Wannan ya biyo bayan hukuncin kotun koli na cewa a cigaba da amfani da tsaffin kudi
  • Lauyoyi da dama sun ce wannan abinda Buhari yayi karan-tsaye ga kotun koli

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya kara wa’adin mayar da tsaffin takardun Naira bankuna da kwanaki 60.

Shugaban kasan ya sanar da hakan yayin jawabin da ya gabatar a safiyar nan daga fadar shugaban kasa.

Buhari ga bayyana cewa ya umurci Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya fitar da tsaffin kudade na N200 saboda mutane su cigaba ca amfani da kudadensu tsawon kwanaki 60.

Amma bai amince a cigaba amfani da tsaffin 500 da 1000 ba, kawai bankunan CBN za’a iya mayarwa.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa Ya Sabawa Kotun koli Wajen Dawo da Tsofaffin N200 Daga Hannun CBN

Buhari
Shugaba Buhari ya kara wa’adin amfani da tsaffin Naira da kwanaki 60 kuma a dawo da tsaffin kudi
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buhari yace:

"Na umurci CBN yayi amfani da dukiyar gwamnati da ya hallata a doka don wayar da kan yan kasa, su samu sabbin kudi cikin sauki kuma mutane su iya kai kudinsu banki."
"Hakazalika na umurci CBN ta hada kai da hukumomin yaki da rashawa don tabbatar da cewa babu wanda yake kokarin yiwa wannan aiki da suke yi zagon kasa."
"Don saukakewa al'ummarmu lamari, na bada izini ga CBN a fito da tsaffin takardun N200 saboda mutane su cigaba da amfani da su tare da sabbin N200, N500, da 500 tsawon kwanaki 60 zuwa ranar 10 ga Afrilu, 2023 da za'a daina amfani da su."
Dukkan tsaffin N1000 da N500 kuma a mayar da su bankin CBN kadai"

Lauya mazaunin jihar Kano, Abba Hikima Fagge, a tsokacinsa kan wannan jawabi ya yi alhini cewa wannan hadari ne ga demokradiyya.

Kara karanta wannan

Muhimman Batutuwa 10 da Aka Fahimta Daga Jawabin Shugaban Kasa Kan Canjin Naira

Yace da ban mamaki yadda ake yiwa kotu mafi girma a Najeriya irin wannan fito-na-fito.

A cewarsa:
"Shugaban kasa da kansa ya tabbatar da cewa wannan lamari na kotu, duk da haka yayi ta kansa wajen fito-na-fito da kotun koli, ta hanyar bada wani umurni sabanin na kotu."
"Wannan raini ne ga kotu mafii girma a Najeriya. Gaskiya an yiwa Demokradiyya mumunar rauni."

Ya kara da cewa:

"Maganar gaskiya shine (itace) irin wannan dimukradiyya bata dace da mu ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel