El-Rufai Ya Bijire Wa Umurnin Buhari, Ya Ce A Cigaba Da Kashe Tsohon Kudi A Kaduna

El-Rufai Ya Bijire Wa Umurnin Buhari, Ya Ce A Cigaba Da Kashe Tsohon Kudi A Kaduna

  • Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya umurci mazauna jiharsa su cigaba da kashe tsaffin takardun naira na N200, N500 da N1000
  • Hakan na zuwa ne bayan Shugaba Buhari ya sanar da cewa tsaffin N500 da N1000 sun dena aiki, sai dai N200 za ta cigaba da aiki zuwa ranar 10 ga watan Afrilu
  • El-Rufai ya yi ikirarin cewa Antoni Janar ya yaudari Buhari ne ya saba umurnin kotun kolin Najeriya da ta ce a cigaba da kashe tsaffin kudin har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci
  • Gwamnan na jihar Kaduna ya yi zargin wannan wani mataki ne da wasu da ke son taya hayaniya a kasa suka dauka, ya kara da cewa za a hukunta duk wanda baya karbar tsohon kudi a Kaduna

Kaduna - Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi watsi da umurin Shugaba Muhammadu kan tsarin sauya sabbin naira, yana mai cewa har yanzu halas ne cigaba da kashe tsaffin kudi a jiharsa.

Kara karanta wannan

Ganduje, El-Rufai Da Wasu Gwamnoni Da Suka Ƙin Bin Umurnin Buhari, Suka Halarta Amfani Da Tsaffin Kudi A Jihohinsu

A jawabin da ya yi a safiyar ranar Alhamis, Buhari ya ayyana cewa daga yanzu an dena amfani da tsaffin N500, da N1000, rahoton Daily Trust.

Gwamna El-Rufai
El-Rufai Ya Bijire Wa Umurnin Buhari, Ya Ce A Cigaba Da Kashe Tsohon Kudi A Kaduna. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Ya umurci yan Najeriya su kai tsaffin kudin CBN da wasu wurare da suka dace.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Amma a jawabin da ya yi wa mutanen jiharsa a daren ranar Alhamis, El-Rufai ya ce har yanzu tsaffin kudin halas ne har sai lokacin da kotun koli ta ce ba haka ba.

El-Rufai: A cigaba da kashe tsaffin kudi a Kaduna, za a hukunta wadanda ba su karbar tsaffin kudin

A cewar gwamnan na Kaduna:

"Don kauce wa shakku, duk tsaffi da sabbin takardun naira za su cigaba da amfani a matsayin halastaccen kudi a jihar Kaduna har sai kotun kolin Najeriya ta yanke hukunci.

Kara karanta wannan

El-Rufai Ya Yarda da Ganduje, Ya Jadadda Kutun-Kutun din da Buhari Yake Shiryawa

"Don haka ina kira ga dukkan mazauna Kaduna su cigaba da amfani da sabbi da tsaffin kudi ba tare da tsoro ba. Gwamnatin Kaduna da hukumominta za ta rufe dukkan hukumomi da suka ki karbar tsaffin kudi kuma ta hukunta masu wurin.
"Idan da bukata, za mu dauki karin mataki bisa doka. Jawabin da shugaban kasa ya yi da farko a safiyar yau (Alhamis) na haramta amfani da tsaffin kudi illa N200 ya saba wa hukunin ranar 8 ga watan Fabrairu wacce kotun koli ta kara tsawaitawa jiya (Laraba)."

Shugaba Buhari ya saba wa umurnin kotun kolin Najeriya, El-Rufa'i

Ya cigaba da cewa:

"Matakin da Antoni Janar na kasa ya dauka na yaudarar shugaban kasa wurin saba umurnin kotun koli ya nuna yada wasu masu wata nufi ke shirin kawo hayaniya a kasa, ta hanyar rashin mutunta hukuncin kotu.
"Matakin na shugaban kasa ya dauka na halasta cigaba da amfani da tsohon N200 har zuwa Afrilu na cikin yarjejeniya da gwamnati ta yi wa gwamnatocin jihohi tayi a wajen kotu kwanaki uku da suka wuce.

Kara karanta wannan

Karancin Kudi: Gwamna Ya Samar Da Bas Din Kyauta Don Ragewa Al'ummarsa Radadin Halin Da Ake Ciki

"Gwamnatin ta ce an yi hakan ne don a riga an lalata tsaffin N500 da N1000. Mun ki amincewa da tayin kuma muka gabatar da hujjar cewa ba a riga an lalata ko takardar manyan kudin daya ba.
"Mun kuma yi imanin cewa tsaffin N200 kawai ba zai isa ya warware wahalhalun da yan Najeriya ke fuskanta ba a kullum. Muna son a bi dukkan umurnin da kotun koli ta bada."

A wani rahoton kun ji cewa tsohon dan majalisar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya yi zargin cewa gwamnoni da ke adawa ta sauyin fasalin kudi ba don kishin talakawa suke yi ba.

Sani, wanda ya yi shekaru hudu a majalisar dattawa ya ce ba su son a canja kudin ne don suna son siyan kuri'u yayin zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel