Ganduje, El-Rufai Da Wasu Gwamnoni Da Suka Ƙin Bin Umurnin Buhari, Suka Halarta Amfani Da Tsaffin Kudi

Ganduje, El-Rufai Da Wasu Gwamnoni Da Suka Ƙin Bin Umurnin Buhari, Suka Halarta Amfani Da Tsaffin Kudi

  • Wasu gwamnonin jihohi sun saba umurnin Shugaba Muhammadu Buhari kan hana amfani da tsaffin N500 da N1000
  • Gwamnonin jihohin Legas, Kaduna da Kano sun umurci mutanensu su cigaba da amfani da tsaffin takardun nairan
  • Jihohin sun dage cewa umurnin da kotun koli na kasa ta bada kan batun shine ya kamata a yi wa biyayya

Duk da umurnin da Shugaba Muhammadu Buhari ya bada a jawabinsa na ranar Alhamis, 16 ga watan Fabrairun 2023, na fada wa yan Najeriya cewa tsohon N200 ne kadai ya halast a kashe har zuwa ranar 10 ga watan Afrilun 2023, wasu gwamnonin jihohi sun fada wa mutanensu su cigaba da amfani da tsaffin N500 da N1000.

Gwamnonin sun ce halas ne a cigaba da kashe tsaffin N500 da N1000 har sai kotun koli ta yanke hukunci kan lamarin a ranar 22 ga watan Fabrairun 2023.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: El-Rufai Ya Bijire Wa Umurnin Buhari, Ya Ce A Cigaba Da Kashe Tsohon Kudi A Kaduna

Tsaffin Naira
Ganduje, El-Rufai Da Wasu Gwamnoni Da Suka Bijire Wa Umurnin Buhari, Suka Halarta Amfani Da Tsaffin Kudi. Hoto: Maksym Kapliuk
Asali: Getty Images

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnoni sun yi watsi da umurnin shugaban kasa

A cewar gwamonin, hukuncin kotun koli ne kadai abin yi wa biyayya.

Idan za a iya tunawa kotun kolin ta umurci CBN ta bari a cigaba da kashe tsaffin nairan tare da sabbi bayan karewar wa'adin ranar 10 ga watan Fabrairu.

A ranar Talata, 14 ga watan Fabrairun 2023, CBN sanar cewa haramun ne amfani da amfani da tsaffin kudi ta bukaci yan Najeriya su mayar da kudaden zuwa rassan ta.

Babban bankin ta kuma bude shafin intanet don yan Najeriya su mayar da tsaffin kudinsu.

Wannan sanarwar ta CBN ta tada hankulan mutane a sassar kasa inda mutane ke ta rububin zuwa banki su kai kudinsu.

Amma gwamnonin jihohi da dama sun dage cewa za su bi umurnin kotun koli kuma sun fada wa mutanen jihohinsu su cigaba da amfani da tsaffin kudin da CBN ta ce an dena amfani da su.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Emefiele Ya Dira Fadar Shugaban Kasa, Ya Bukaci A Bi Umurnin Buhari Kan Sauyin Naira

Har yanzu hukuncin kotun koli yana nan daram-dam, Antoni Janar na Legas

Bayan jawabin Buhari, Antoni Janar na Legas kuma kwamishinan shari'a Moyosore Onigbanjo ya ce har yanzu hukuncin kotun kolin kan sauya fasalin nairan yana nan daram-dam.

Onibanjo ya ce gidajen mai, bankuna, da sauran hukumomi da ke saba umurnin kotun kolin za su iya fuskantar hukunci.

The Punch ta rahoto cewa Onibanjo ya bayyana hakan ne a shirin Business Show na TVC a ranar Alhamis 16 ga watan Fabrairu bayan jawabin Buhari.

Gwamnan Kaduna ya bijire wa umurnin Buhari na haramta amfani da tsaffin N500 da N1000

Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai shima ya ayyana cewa halas ne a cigaba da kashe tsaffin kudin a jiharsa har sai lokacin da kotun koli ta ce ba haka ba.

A cewar rahotanni, El-Rufai ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi wa jihar a ranar Alhamis, 16 ga watan Fabrairu bayan jawabin Buhari.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa Ya Sabawa Kotun koli Wajen Dawo da Tsofaffin N200 Daga Hannun CBN

Kano ta dage kan hallarcin tsaffin nairorin

Duk da jawabin da Buhari ya yi na dena amfani da tsaffin N500 da N1000, gwamnatin jihar Kano ta ce za ta hukunta duk wani banki, da kamfani ko kasuwanci da masu POS da ke kin karbar tsaffin naira.

Gwamnan na Kano ya bada umurnin kama masu kantina da suke kin karbar tsaffin kudi.

A wani rahoton kun ji cewa Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya yi barazana rufe duk wani banki da ba ya karbar tsohon kudi.

Gwamnan ya soki umurnin hana amfani da tsaffin kudin yana mai cewa zalunci ne tunda babu sabbin kudin isasu a gari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel