Emefiele Ya Isa Villa, Ya Bukaci A Bi Umurnin Buhari Kan Sauyin Naira

Emefiele Ya Isa Villa, Ya Bukaci A Bi Umurnin Buhari Kan Sauyin Naira

  • Mr Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin kasa, CBN, ya ziyarci fadar Aso Villa a safiyar ranar Alhamis 16 ga watan Fabrairu
  • Emefiele ya ce ya yi taro da shugabannin bankunan kasuwanci a kalla guda 15 a kasar ya kuma yi kira ga al'umma su bi sabon umurnin da Shugaba Buhari ya bada
  • Buhari, a sanarwar da aka haska a gidajen talabijin na kasar ya ce an halasta cigaba da tsohon N200 har zuwa ranar 10 ga watan Afrilun 2023 don saukaka karancin naira

FCT Abuja - Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele, a ranar Alhamis, ya ce ya gana da shugabannin a kalla bankunan kasuwanci 15 tun bayan umurnin da Shugaba Muhammadu Buhari ya bada na baya-bayan nan kan tsarin sauyin naira.

Ziyarar ta Emefiele tana zuwa ne awanni bayan shugaban kasa, cikin wata sako da aka fitar a gidajen talabijin ya ce tsohuwar takardar N200 ne kawai za a cigaba da amfani da ita har ranar 10 ga watan Afriliun 2023.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa Ya Sabawa Kotun koli Wajen Dawo da Tsofaffin N200 Daga Hannun CBN

Emefiele da Buhari
Emefiele Ya Isa Villa, Ya Bukaci A Bi Umurnin Buhari Kan Sauyin Naira. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ziyarar Emefiele zuwa Villa ba ta da alaka da ganin Shugaba Buhari

An rahoto cewa gwamnan na CBN ya tafi fadar shugaban kasar ne don wata bukata ta daban (ba ganawa da shugaban kasa ba.)

The Punch ta rahoto a baya cewa a ranar Laraba Buhari ya ce tsaffin takardun naira na N500 da N1000 sun dena aiki a kasar.

Amma, ya ce tsohon N200 zai cigaba da amfani har zuwa ranar 10 ga watan Afrilun 2023, yayin da ya yi kira ga yan Najeriya zu mayar da tsaffin N500, da N1000 a CBN.

Shugaban kasar ya tabbatarwa al'ummar kasa cewa an dauki matakin sauya fasalin kudin ne domin inganta tattalin arziki, tsaro da toshe matsaloli da ke tasowa sakamakon amfani da kudaden haram, ya kara da cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba na sauke nauyin da ya rataya kansa na kiyaye kasar.

Kara karanta wannan

Muhimman Batutuwa 10 da Aka Fahimta Daga Jawabin Shugaban Kasa Kan Canjin Naira

Gwamnan Jihar Ogun ya yi barazanar rufe bankunan da ba su karbar tsaffin kudi a jiharsa

A baya kun ji cewa Dapo Abiodun, gwamnan jihar Ogun ya ce zai rufe duk wani banki da baya karbar tsaffin takardun naira daga mutane, Daily Trust ta rahoto.

Ya furta hakan ne a ranar Talata 14 ga watan Fabrairu yayin da ya ke yi wa yan kasuwa mata da maza jawabi a kasuwar Itoku Kampala a garin Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel