Zan Rufe Dukkan Bankunan Da Ba Su Karbar Tsaffin Kudi A Jiha Ta, Gwamna Abiodun

Zan Rufe Dukkan Bankunan Da Ba Su Karbar Tsaffin Kudi A Jiha Ta, Gwamna Abiodun

  • Gwamnan Ogun ya gargadi bankuna da cewa zai rufe duk wani banki da ya ki karbar tsohon kudi
  • Gwamnan ya kuma ce dole ne su ci gaba da karbar kudin tunda dai babu sabon kudaden a hannun al'umma
  • Harkokin kasuwanci sun tsaya biyo bayan zanga-zangar da wasu fusatattun mutane suka yi a yan Sango-Ota da ke jihar

Jihar Ogun - Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya yi barazanar rufe duk wani bankin kasuwanci da ke kin karbar tsohon kudi, rahoton Daily Trust.

Hakan ya biyo bayan rahoton haramta kudin da wasu bankuna, mutane da kuma yan kasuwa biyo bayan karewar wa'adin 10 ga watan Fabrairu da babban bankin kasa ya bayar.

Dapo Abidoun
Za'a Rufe Dukkan Bankunan Da Ke Kin Karbar Tsaffin Kudi A Ogun. Hoto: Leadership
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

ATM na ba da tsoffin Naira: Jama'a sun mamaye CBN, 'yan sanda sun mamaye kawo dauki

Gwamnan ya bayyana haka a ranar Talata lokacin da yake jawabi ga yan kasuwa maza da mata a kasuwar Itoku Kampala a Abeokuta, a wani salon yakin neman zaben tazarce.

Gwamna Abiodun ya soki bankuna kan dena karbar tsaffin kudi

Abiodun, wanda ya yi tir da hukuncin bankunan, ya ce tunda babu sababbin kudin, dole ne bankuna su cigaba da karbar tsoho don saukakawa al'umma.

Ya yi kira ga mutane da su kwantar da hankali, yana bada tabbacin gwamnatin sa na aiki tukuru don shawo kan lamarin, rahoton Leadership.

A gefe guda, harkokin kasuwanci sun samu nakasu a ranar Talata biyo bayan zanga-zanga da wasu fusatattun mutane suka yi saboda karancin takardun sababbin N200, N500, da kuma N1000 a Sango-Ota, karamar hukumar Ado-Odo/Ota ta Jihar Ogun.

Mazauna yankin da suka dinga zariya zuwa banki amma sun kasa cirar kudin su. An ruwaito cewa al'ummar sun fusata ne lokacin da aka ki karbar tsofaffin kudin su da suka kai ajiya.

Kara karanta wannan

Mafita ta samu, CBN ya fadi hukuncin da zai yiwa masu POS da ke karbar sama da N200

Al'umma sun yi zanga-zangan kan kin karbar tsaffin kudi

A ranar Talata, masu zanga-zangar sun cika shataletalen Joju na titin Idiroko-Ota, wanda ya jawo cinkoson ababen hawa.

Bayan kone-kone a titi, mutanen sun soki gwamnatin Buhari, da zargin APC da gallazawa talakawa. An tura yan sanda don su kula da ma'aikatan banki a Sango-Ota.

In za a iya tunawa ko a satin da ya gabata anyi gagarumar zanga-zanga a Abeokuta, inda aka kai hari kan bankuna tare da harbin mutum daya

Yan kasuwa, bankuna da gidajen suna dena karbar tsaffin kudi a Sokoto

A baya kun ji cewa wasu yan kasuwa da bankuna da gidajen mai suna fara kin karbar tsohon kudi a jihar Sokoto.

Hakan ya faru ne biyo bayan cikar wa'adin da babban bankin kasa ya bada na dena amfani da tsohon kudin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel