'Yan Ta’addan Boko Haram Na Shirin Kai Hari Kan Jirgin Kasan Abuja Zuwa Kaduna, Inji Hukumar DSS

'Yan Ta’addan Boko Haram Na Shirin Kai Hari Kan Jirgin Kasan Abuja Zuwa Kaduna, Inji Hukumar DSS

  • Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gano wani boyayyen shirin 'yan ta'addan Boko Haram a kwanakin nan
  • An ce 'yan ta'adda sun shirya kai hari kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, ma'aikatan sufuri ta ankara
  • A shekarar da ta gabata ne 'yan ta'adda suka farmaki al'umma a cikin jirgin kasan na Abuja zuwa Kaduna

FCT, Abuja - Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta bankado wani shiri na kungiyar ta’addanci ta Boko Haram na kai hari kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a kwanaki kadan masu zuwa.

Ma’aikatar sufuri ta Najeriya a cikin wata wasika da ta aikatawa ma’aikatar tsaro da Daily Trust ta samu a ranar Alhamis ta ce, a ranar 1 ga watan Faburairu DSS ta aika sakon barazanar da ta hango na kai harin ‘yan ta’addan.

Kara karanta wannan

An shiga firgici yayin da mata mai tabin hankali a Kano ta jefa jaririyarta a masai

Ma’aikatar sufuri ta yi kira ga ma’aikatar tsarin Najeriya da ta duba lamarin cikin gaggawa tare da kiran taron masu ruwa da tsaki don dubawa da tsara yadda za a dakile harin.

Hukumar DSS ta ce 'yan ta'adda na shirin kai hari kan jirgin kasan Abuja-Kaduna
'Yan Ta’addan Boko Haram Na Shirin Kai Hari Kan Jirgin Kasan Abuja Zuwa Kaduna, Inji Hukumar DSS | Hoto: saharareporters.com
Asali: UGC

Yadda aka sace mutane da yawa a jirgin kasan Abuja-Kaduna

Idan baku manta ba, a ranar 28 ga watan Maris din 2022 ne ‘yan ta’adda suka kai hari kan jirgin kasan na Abuja zuwa Kaduna, inda suka hallaka mutane da yawa, suka sace wasu tare da raunata adadi mai yawa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A hankali, daki-daki aka sako mutanen da aka sace, wanda na karshe aka sako mutum 23 a watan Oktoban bara bayan shafe watanni shida a hannun ‘yan ta’addan, SaharaReporters ta ruwaito.

Kwamitin shugaban kasa karkashin jagorancin hafsun sojin Najeriya, Janar Lucky Irabor ne ya yi aiki wajen tabbatar da sako mutanen 23 daga hannun ‘yan ta’adda.

Kara karanta wannan

Karfin hali: EFCC ta kama shugabanta na bogi, ya damfari mutane kudi masu yawa

Yadda aka fara sako su

A tun farko, an sako mutum 11 a watan Yunin 2022 yayin da aka sako wasu bakwai a watan Yulin shrkarar, ciki har da Sadiq, dan shugaban zauren dattawan Arewa (NEF), Angi Abdullahi.

A ranar 2 ga watan Agusta, an sako wasu mutum biyar, inda daga baya aka samu nasarar samun wasu adadi da aka sako.

Ana zargin, an biya ‘yan ta’addan kudaden fansa masu yawa kafin su sako mutanen da suka sace a watannin na baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel