NNPC Ya Sanar Da Ranar Da Zai Fara Hakar Danyen Man Fetur A Nasarawa

NNPC Ya Sanar Da Ranar Da Zai Fara Hakar Danyen Man Fetur A Nasarawa

  • Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPP, ya sanar da cewa zai fara hako man fetur a rijiyar Keana da ke jihar Nasarawa
  • Mele Kyari, shugaban NNPP na kasa ne ya furta hakan yayin da ya ziyarci Gwamna Abdullahi Sule na jihar ta Nasarawa
  • Kyari ya ce idan har aka dace wurin hako man, abin da za a samu sai kawo alheri sosai ga al'ummar garin da jihar Nasarawa

Lafiya, Nasarawa - Kamfanin haka da tace man fetur na Najeriya, NNPC, ya sanar da shirinsa na fara hakar danyen man fetur a jihar Nasarawa a ranar 21 ga watan Maris na 2023.

Shugaban kamfanin na NNPC Limited, Mele Kyari, ne ya sanar da hakan yayin ganawarsa da Gwamna Abdullahi Sule a garin lafiya, ranar Alhamis, rahoton The Punch.

Mele Kyari
Labari Mai Dadi: NNPC Ta Sanar Da Ranar Da Za Ta Fara Hakar Mai A Nasarawa. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Karancin Kudi: Gwamna Ya Samar Da Bas Din Kyauta Don Ragewa Al'ummarsa Radadin Halin Da Ake Ciki

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Naira Metric ta rahoto yana cewa:

"Dole a yi wannan aikin cikin gaggawa saboda duniya tana fara kauracewa makamashi na man fetur saboda sauyi zuwa makamashin zamani, zai fi alheri idan ka shiga kasuwar da wuri.
"Idan ba haka ba, nan da shekara 10, babu wanda zai yarda ya saka kudinsa a harkar kasuwanci na man fetur idan dai ba daga ribar ka bane."

Ya cigaba da cewa hadin kai daga mutanen gari da dokoki da suka dace na da muhimmanci don kare afkuwar irin abubuwan da suka faru a Neja Delta.

Idan aka yi nasara, mutanen Nasarawa za su amfana sosai, Kyari

Kyari ya ce idan har aka yi nasara a rijiyar Keana, za ta iya sauya rayuwar mutanen jihar baki daya.

Kamfanin na NNPP a cikin wata takarda, ta ce tana fatan samun man fetur a wurare da dama a arewa, ciki har da Nasarawa bayan gano man a Bauchi da Gombe.

Kara karanta wannan

Bayan Wike, Bola Tinubu Ya Lallaɓa Wurin Wani Gwamnan PDP Ana Dab da Zaɓen 2023

Kamfanin man na kasa ta ce tana daukan matakan da suka dace domin neman man a arewa, a matsayin mataki na fadada mai da kasar ke samu.

Baya ga arewa, NNPP ta ce tana bincike na neman man fetur din a yankin Anambra.

NNPP ta sanar da cewa an gano man fetur a arewa maso gabas

A wani rahoton kun ji cewa hukumar NNPP ta bayyana cewa an gano danyen man fetur a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Samson Makoji, mukadashin shugaban sashin hulda da mutane na kamfanin ne ya bada sanarwar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel