Yanzu-yanzu: An gano man fetur a yankin arewa maso gabas - NNPC

Yanzu-yanzu: An gano man fetur a yankin arewa maso gabas - NNPC

Hukumar Kamfanin Man Fetur ta Najeriya (NNPC) ta sanar da cewa an gano mai a yankin arewa maso gabashin kasar.

The Cable ta ruwaito cewa mukadashin manajan sashin hulda da al'umma na kamfanin, Samson Makoji ne ya bayar da wannan sanarwar a ranar Juma'a.

Ya ce gano man fetur da iskar gas masu yawa da akayi a yankin Gongola "zai janyo masa saka hannun jari zuwa kasar kuma zai samar wa al'umma ayyukan yi da inganta kudaden shiga da gwamnati ke samu."

Sanarwar ta ce, Hukumar NNPC tana sanar da gano bakin mai masu yawa a Rafin Kolmani II da Upper Benue Trough, Gongola Basin a yankin arewa maso gabashin kasar.

DUBA WANNAN: Tausayi: Bidiyon yadda Sarki Sanusi ya zubar da hawaye yayin bayar da labarin wata mata a Kano

Idan ba a manta ba shugaba Muhammadu Buhari ne ya kaddamar da fara hakar mai a rafin Kolmani II a ranar 2 ga watan Fabrairun 2019.

Makoji ya yi bayanin cewa an haka daya daga cikin rijiyoyin har sai da ya kai zurfin kasa 13,701 wadda hakan yasa aka gano man fetur da iskar gas a matakai daban-daban.

Ya ce a ranar Alhamis, daya daga cikin ma'ajiyarsu ta fashe kuma, 'bakin mai ya fara ambaliya misalin karfe 9.20 na dare wadda hakan yasa aka kone gas din da ke ciki domin kare afkuwar matsala a wurin hakar man."

Makoji ya ce NNPC za ta yi amfani da sabbin dabaru na zamani domin kiyaye haddura da za a iya haduwa da su inda ya kara da cewa kamfanin na shirin fara hakkan wasu rijiyoyin a Gongola Basin.

Ya kuma ce za a mayar da hankali da yankunan da ake kira Dahomey da Anmbra Basin da tuni an samu man fetur da iskar gas a wurin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel