Yar Najeriya Da Ke Aikin Kanikanci Ta Koma UK Da Zama, Bidiyonta Ya Yadu

Yar Najeriya Da Ke Aikin Kanikanci Ta Koma UK Da Zama, Bidiyonta Ya Yadu

  • Wata matashiyar budurwa yar Najeriya da ke aikin kanikanci ta koma kasar Birtani da zama inda ta mallaki digiri na biyu
  • Matashiyar ta wallafa wani bidiyo a TikTok wanda ke kunshe da hoton lokacin da take aiki a matsayin bakanike a Najeriya
  • Masu amfani da TikTok da labarinta ya burge su sun je sashin sharhi don jinjina mata kan jajircewarta

Wata yar Najeriya da ke aikin kanikanci a shekarun baya ta koma kasar Birtaniya inda take rayuwa a yanzu.

A ranar 15 ga watan Fabrairu, matashiyar mai suna Feesah Oman ta wallafa wani bidiyo a TikTok don bayar da labarin rayuwarta zuwa yanzu.

Matashiya mai aikin kanikanci
Yar Najeriya Da Ke Aikin Kanikanci Ta Koma UK Da Zama, Bidiyonta Ya Yadu Hoto: @feesah_oman.
Asali: TikTok

Hoton farko a bidiyon ya nuno lokacin da take aiki a matsayin bakanike yayin da take a gida Najeriya.

Matashiya ta koma Birtani bayan ta yi aiki a matsayin bakanike

Kara karanta wannan

Zabin Allah Na Bi: Bidiyon Soyayya Da Wata Kyakkyawar Mata Da Mijinta Mai Nakasa Ya Tsuma Zukata

Sai wani hoto da ke nuna lokacin da ta kammala bautar kasarta (NYSC) ya biyo baya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ana nan sai ta yi aure sannan ta haifi yara biyu, bayan nan suka koma kasar Birtaniya tare da mijinta.

Wani abun farin ciki a rayuwarta shine cewa ta mallaki digiri na biyu a fannin kula da lafiya daga jami'ar Coventry, UK.

Labarin nasarar da ta samu a rayuwa zuwa yanzu ya taba mutane da dama a TikTok.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Dannie ta ce:

"Ban san ki ba amma ina matukar alfahari da ke."

@Sumaiya ta yi martani:

"Ina rokon Allah ya mun irin ya taki."

@VinzCollections ta ce:

"Abun dariya yadda ta ke sanye da takalmin NYSC a hoton farko."

@Adetunji ololade Fathia rta yi martani:

"Ina kokarin gina rayuwa ta wannan."

Kara karanta wannan

Kai Mummuna Ne: Budurwa Ta Kunyata Saurayi, Ta Ki Amincewa Ta Aure Shi, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

@Anyanwu Ijeoma Peace ta ce:

"Ma shaa Allah hakan ya yi kyau, na taya ki murna."

Hazikin dan Najeriya ya kera rishon girki mai amfani da batura

A wani labarin, mun ji cewa wani fasihin dan Najeriya ya ba da mamaki a soshiyal midiya bayan ya kera wani rishon girki da ke amfani da batura wanda ka iya kawo sauki ga jama'a a wannan lokaci da ake ciki.

Mutumin ya ce idan mutum ya saka baturan, zai iya daukarsa tsawon makonni biyu kafin su yi sanyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel