Dan Najeriya Ya Kera Rishon Girki Mai Amfani Da Batir, Bidiyon Ya Yadu

Dan Najeriya Ya Kera Rishon Girki Mai Amfani Da Batir, Bidiyon Ya Yadu

  • Wani hazikin mutumin Najeriya ya yi nasarar kera rishon girki da ke amfani da batura kawai
  • A wani bidiyo da ya yadu a TikTok, mutumin ya nuna yadda za a yi amfani da rishon kuma kowa ya jinjina masa
  • Legit.ng ta yi nasarar tuntubar makerin rishon kuma ya bayyana sunansa a matsayin Ndubuisi Okoye

Wani mutumin Najeriya ya kera rishon girki wanda ke amfani da batura kawai da wani dan fanka.

Mutumin mai suna Ndubuisi Okoye wanda ya fito daga yankin Amagunze a jihar Enugu ya nunawa jama'a yadda ake aiki da rishon kuma an nadi jawabin nasa a wani bidiyo da @thetiktoktroublemaker ya wallafa a TikTok.

Dan Najeriya da rishon girki
Dan Najeriya Ya Kera Rishon Girki Mai Amfani Da Batir, Bidiyon Ya Yadu Hoto: @thetiktoktroublemaker.
Asali: TikTok

A bidiyon, Ndubuisi wanda ke da risho da dama ya bajewa jama'a su don ganin abun da ya kirkira.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: El-Rufai ya fadi abu 1 da gwamnoni 36 suka roki Buhari ya yiwa talakawa

Bidiyon risho mai amfani da batura

An jera baturan a wani dan kusuwa da aka tanada sannan aka hada shi da wata waya zuwa wanda ke jikin rishon.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da aka daura tukunya da ruwa ciki a kan rishon, sai ga shi ya fara tafasa. Mutanen da ke wajen sun cika da mamaki. Yana kuma aiki da lantarki.

Da yake bayanin yadda rishon zai taimakawa gidaje idan babu lantarki, mutumin ya ce rishon na aiki da tsoffin batura.

A cewarsa, baturan na iya shafe tsawon makonni biyu kafin su daina aiki gaba daya.

Yadda rishon ke aiki da fanka

Legit.ng ta tattauna da Ndubuisi kuma ya ce rishon na zuwa da wani fanka. A cewarsa, yana bukatar gawayi domin ya yi aiki. Sai dai kuma, fasahar shine cewa fankar na taimakawa wajen kada wutan sosai da rishon don girki ya yi sauri.

Kara karanta wannan

A ina kika samo: Kowa girgiza, wata mata ta samo damin kudi, tana siyar da N50k a farashin N60k

Kalamansa:

"Za ka sa gawayi kadan a ciki. Ina saka fanka a ciki, kuma idan babu wuta, za ka iya amfani da batir. Fankar na sa wutan ya tashi da sauri."

Ndubuisi ya fadama Legit.ng cewa shekarunsa 48 kuma cewa yanzu haka yana Onitsha inda ya halarci kwalejin fasaha.

A cewarsa, karamin rishon ana siyar da shi kan N7000 yayin da babban yake kan N12000. Ya ce yana bukatar kudi domin bunkasa shi.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@user7615872546220 ya ce:

"Yallabai ya yi bidiyo da kyau, gaskiya ina bukatar wannan kaya."

@cent Paul:

"Aiki ya yi kyau matuka."

@Berryboiy ya tambaya:

"Zai iya dafa wake?"

Matashi ya kera katafaren gado da bulo

A wani labarin kuma, wani matashi ya raba kansa da wulakancin kafinta inda ya kera wani katafaren gado da bulo da siminta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel