Ba ka Hadu ba: Budurwa ta Tozarta Saurayin Da Ya Bukaci Ta Auresa a Ranar Masoya

Ba ka Hadu ba: Budurwa ta Tozarta Saurayin Da Ya Bukaci Ta Auresa a Ranar Masoya

  • Bikin ranar masoya ta 2023 ta zo ma wani matashi ta hagu yayin da budurwar da yake so ta ki amsar tayin aurensa
  • Baya ga kin amsar tayin aurensa, matashiyar ta kuma kunyata shi a bainar jama'ar da suka taru
  • Jama'a sun yi cece-kuce kan bidiyon yayin da wasu masu amfani da soshiyal midiya ke ganin shiri kwaikwayo ne

Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta kunyata wani matashi yayin da ta ke karbar tayinsa na neman aurenta a ranar masoya.

An gano bidiyon lamarin wanda ya afku a harabar jami'ar Babcock da ke Ilishan-Remo, jihar Ogun a manhajar TikTok.

Saurayi da budurwa
Ba Ka Da Kyau: Matashiya Ta Ki Amsar Tayin Auren Saurayi a Ranar Masoya Ta Duniya, Ta Kaskanta Shi a Bidiyo Hoto: @yohwilly
Asali: TikTok

A bidiyon, an gano mutumin duke a kan gwiwowinsa yana fuskantar matashiyar dauke da zobe a hannusa yayin da yake bukatar ta aure shi.

Kai tsaye matashiyar ta ki yarda da bukatarsa yayin da ta yi masa ba'a da tozarta shi. Ta ce bai da kyawun fuska, bai da kudi sannan kuma ita ba ajinsa bace.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Matashi Ya Je Banki Da Ruwa a Bokiti, Ya Yi Wanka Yayin da Mutane Ke Kallonsa a Bidiyo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta karbe zoben daga hannunsa sannan ta jefe shi da shi, yayin da ta kuma tarwatsa wani kunshin kyauta da ya kawo mata a kwali. Wannan ya saka taron jama'ar zikin wani hali.

Mutane da dama basu yarda da bidiyon ba inda suka ce shirin kwaikwayo ne.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Yilson Acquaye ta ce:

"Ba su ma iya wasan kwaikwayo ba."

pere ya ce:

"Ia da take magana ta ma kalli kanta a madubi kuwa da take cewa wani haka mtcheww."

Folorunsho Helen ta ce:

"Wannan shirin wasan kwaikwayo ne."

Danilove ta ce:

"Daga baya yarinyar za ta nemi miji ba za ta samu ba. Taimakonta gayen ke son yi amma bata sani ba."

Ayo Mi ya ce:

"Za ka je neman auren mutumin da bai ci ya koshi ba."

ŽÖFT ya ce:

Kara karanta wannan

Bidiyon Kyakkyawar Gurguwa Tana Tikar Rawa Da Kafa Daya Cike da Kwarewa Ya Ba Da Mamaki

"Ba za ta taba samun miji ba kuma koda ta samu mutumin da zai dunga dukanta ne kullun."

Kyakkyawar matashiya mai kafa daya ta burge jama'a da salon rawanta

A wani labarin, jama'a sun mato a soshiyal midiya bayan su ci karo da bidiyon wata kyakkyawar matashiya mai kafa daya tana kwasar rawa cike da farin ciki da annashuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel