Kotun Koli Ta Dage Shari’ar CBN da Gwamnonin Najeriya 12 Kan Batun Fasalin Kudizuwa 22 Ga Fabrairu
- A zaman ranar Laraba 15 Faburairu, 2023, kotun koli ya dage ci gaba da sauraran shari’ar da aka shigar kan CBN da gwamnatin Najeriya
- Gwamnonin Arewa sun maka gwamnatin tarayya da Babban Bankin Najeriya (CBN) a kotu kan batun sauya fasalin kudi
- Sun koka da yadda talakawan jihohinsu ke fama da matsaloli bisa wa’adin da CBN ya sa na daina amfani da tsoffin N200, N500 da N1000
FCT, Abuja - Kotun koli a Najeriya ta dage karar da aka shigar gabanta kan kudurin CBN ta tsawaita wa’adin daina amfani da tsoffin kudi a kasar.
Babban Bankin Najeriya ya sauya fasalin N200, N500 da N1000, ya ce daga ranar 10 ga watan Faburairu tsoffi sun daina aiki, Channels Tv ta ruwaito.
Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna, Yahaya Bello na Kogi da Bello Matawalle na jihar Zamfara sun ce ba za ta sabu ba, sun kai kara kotu.
A zaman ta na baya, kotun ta ce a ci gaba da amfani da tsoffin kudi har zuwa ranar 15 ga wata, wato yau kenan don ya sake sauraran karar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An kara adadin jihohin da ke kalubalantar CBN
Jihohi da yawa a kasar nan sun nuna sha’awar shiga jerin wadanda ke kalubalantar gwamnatin, inda suka amince da ra’ayin jihohin uku na sama.
A zaman na yau, mai shari’a John Okoro ne ya jagoranci alkalai bakwai na kotun koli don sake sauraran karar, Punch ta ruwaito.
Ya ce, kotun ba za ta yi biris da karar ba da manufarta kasancewar ta shafi yadda ‘yan kasa ke shan wahala.
Tuni alkalan suka amince da shigar da karin jihohi tara da ke sha’awar shiga shari’ar, kuma ya dage ci gaba da zama zuwa 22 ga watan Faburairu 2023.
Karancin kudi zai shafi zaben 2023
A wani labarin kuma, kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ya koka da cewa, karancin kudi zai shafi aikin zaben 2023.
Ya bayyana cewa, akwai ma'aikatan da dole sai an ba su kudade a hannu kafin iya tafiya rumfunan zabe a kasar.
Hakazalika, ya ce ya kamata CBN ya duba tare da warware matsalar da ta addabi kusan kowa a kasar.
Asali: Legit.ng