Gwamnatin Tarayya da CBN Basu Saba Umarnin Kotun Koli Ba, Fadar Shugaban Kasa Ta Magantu Kan Musayar Kudi

Gwamnatin Tarayya da CBN Basu Saba Umarnin Kotun Koli Ba, Fadar Shugaban Kasa Ta Magantu Kan Musayar Kudi

  • Gwamnatin Buhari ta magantu game da halin da ake ciki na batun sauyin kudi da daina amfani da tsoffin Naira
  • Fadar shugaban kasa ta ce, bata saba ka’ida ba, hakan CBN bai saba umarnin kotun koli ba kan batun Naira
  • A hannu guda, ana ci gaba da ganin laifin CBN lan saba umarnin kotun koli na cewa a ci gaba da kashe tsoffin Naira

FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta yi da zargin da ake cewa, gwamnatin tarayya da babban bankin Najeriya (CBN) sun saba umarnin kotun koli game da batun sabuwar dokar musayar kudi.

Ku tuna Legit.ng Hausa ta tattaro cewa, kotun koli a makon da ya gabata ta ba da umarni ga CBN da ya dakatar da batun kawo karshen wa’adin daina amfani da tsoffin kudi zuwa 10 ga watan Faburairu.

Kara karanta wannan

ATM na ba da tsoffin Naira: Jama'a sun mamaye CBN, 'yan sanda sun mamaye kawo dauki

Kotun ya yanke cewa, za a ci gaba da karbar tsoffin kudade hade da sabbi har zuwa ranar 15 ga watan Faburairu.

Ba mu sabawa umarnin kotun koli ba
Gwamnatin Tarayya da CBN Basu Saba Umarnin Kotun Koli Ba, Fadar Shugaban Kasa Ta Magantu Kan Musayar Kudi | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Duk da haka, wasu bankuna da ‘yan kasuwa a Najeriya sun daina karbar kudin tun ranar Litinin, 13 ga watan Faburairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, CBN ya ce babu bukatar sake kara wa’adin daina amfani da kudin kamar yadda wasu ‘yan Najeriya ke bukata.

Bamu saba umarnin kotun koli ba, fadar shugaban kasa

A bangare guda, wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar ta ce, gwamnatin Buhari da CBN basu saba umarnin kotun ba.

A cewar Garba Shehu, har yanzu gwamnati na kan taraddudi kan batun kudin, kuma za ta fitar da matsaya bayan umarnin kotu, ahoton Leadership.

A cewarsa:

“Matsayar gwamnati da na CBN za ta bayyana bayan yanke hukunci kan shari’ar a gobe (Laraba).”

Kara karanta wannan

Mafita ta samu, CBN ya fadi hukuncin da zai yiwa masu POS da ke karbar sama da N200

Kotunan jihar Legas sun daina karbar tsoffin Naira duk da umarnin kotun koli

A wani labarin kuma, kun ji yadda kotuna a jihar Legas suka kauracewa tsoffin takardun Naira a cikin makon nan.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da CBN yace wa’adin daina amfani da tsoffin kudi ya kare a kasar.

‘Yan Najeriya na ci gaba da fuskantar karancin kudi, musamman a bankuna da wurin masu POS.

Asali: Legit.ng

Online view pixel