'Yan Sanda Sun Mamaye CBN Na Ondo Yayin da Fusatattun Jama’a Suka Yi Masa Kawanya

'Yan Sanda Sun Mamaye CBN Na Ondo Yayin da Fusatattun Jama’a Suka Yi Masa Kawanya

  • ‘Yan sanda sun mamaye CBN a jihar Ondo saboda an ki ba mutane damar su shiga don adana tsoffin kudadensu da suka tara
  • CBN ya ce an daina amfani da tsoffin kudi N200, N500 da N1000 a Najeriya, za a ci gaba da kashe sabbin da aka buga kwanan nan
  • Jama’a sun koka cewa, har yanzu bankuna na ci gaba da ba da tsoffin kudi ga mutane, musamman a injunan POS na jihar Ondo

Jihar Ondo - ‘Yan sanda dauke da makamai sun mamaye harabar Babban Bankin Najeriya (CBN) da ke Alagbaka a garin Akure na jihar Ondo biyo bayan yadda jama’a suka yiwa bankin kawanya.

Daily Trust ta ruwaito cewa, wasu fusatattun kwastomomi da sanyin safiyar ranar Talata sun mamaye ofishin CBN na jihar saboda bankunan kasuwanci sun ki karbar tsoffin kudadensu.

Kara karanta wannan

Mafita ta samu, CBN ya fadi hukuncin da zai yiwa masu POS da ke karbar sama da N200

Kwastomomin da suka hada da ‘yan acaba, ‘yan kasuwa, ma’aikatan gwamnati da mata sun yiwa bankin kawanye ne domin a sauya musu tsoffin kudadensu zuwa tsoffi.

Yadda 'yan sanda suka mamaye bankin CBN na Ondo
'Yan Sanda Sun Mamaye CBN Na Ondo Yayin da Fusatattun Jama’a Suka Yi Masa Kawanya | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Wasu daga cikin kwastomomin sun bayyana cewa, bankunan kasuwanci sun daina karbar tsoffin kudade tun ranar Litinin da kuma safiyar ranar Talata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yawan kwastomin sun yi cincirindo zuwa bankunan kasuwanci da ke yankin domin cire sabbin kudi, amma lamarin ya gagara.

Bankuna na ci gaba da ba tsoffin kudi

Sun bayyana kokensu da cewa, har yanzu injunan ATM a bankunan kasuwanci na ci gaba da ba da tsoffin kudade, New Telegraph ta tattaro.

A cewar wani daga cikin kwastomomin da suka fusata:

“Ku duba fa, bankuna ba sa karbar tsoffin kudi daga hannunmu. Sun umarce mu da mu tafi mu kai kudin ofishin CBN wannan ne yasa muka zo nan yanzu.

Kara karanta wannan

Masu Zanga-Zanga Sun Mamaye CBN Kan Sabuwar Sanarwar Da Emefiele Ya Fitar Kan Tsoffin Kudi, Bidiyo

“Abin takaici, wadannan bankunan na ci gaba da ba my tsoffin kudaden da su kansu ba sa karba ko da wasa. Abin babu dadi.”

Wani ma’aikacin CBN ya shaidawa majiya cewa, nan kusa babban bankin zai fitar da sanarwar a ci gaba da karbar tsoffin kudade a bankunan kasuwanci.

Kotu ya ki karbar tsoffin Naira

A wani labarin kuma, kun ji yadda kotunan jihar Legas suka ki karbar tsoffin Naira duk da cewa kotun koli ta ce a ci gaba da kashe kudaden.

Gwamnonin Arewa sun maka gwamnatin Tarayya a kotu kan batun da ya shafi sauya fasalin Naira da kawo sabbin kudi.

Alamu sun nuna an samu sabani tsakanin bankin CBN da sauran bankuna da kuma wasu daga cikin hukumomin gwamnatin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel