Bankuna a Wasu Jihohi Sun Ki Bin Umarnin CBN, Suna Ci Gaba da Ba Tsoffin Kudi

Bankuna a Wasu Jihohi Sun Ki Bin Umarnin CBN, Suna Ci Gaba da Ba Tsoffin Kudi

  • Babban Bankin Najeriya na ci gaba da ganin abubuwa mara dadi daga bankunan kasar nan na kasuwanci
  • Wannan na faruwa ne kasancewar bankunan sun gaza ba kwastomominsu sabbin kudade a injunan POS
  • 'Yan kasuwa na ci gaba da shiga damuwa kasancewar ba sa samun wadatattun sabbin kudade a bankunan kasar

Najeriya - Duk da umarnin da CBN ya ba bankunan kasar nan kan su daina zuba tsoffin kudade a ATM, su ke zuba sabbi, har yanzu wasu bankunan na ci gaba da ba da tsoffin kudi.

Idan baku manta ba, CBN ya umarci ‘yan Najeriya da su daina karbar tsoffin kudi idan bankunan kasar suka ba su saboda rage yaduwarsu tun yanzu.

CBN ya sanya wa’adin daina amfani da tsoffin kudin daga ranar 31 ga watan Janairun da muke ciki.

Kara karanta wannan

Ana Saura Kwana 11 Tsoffin Kudi su Zmaa Takardun Tsire, Bankuna na Cigaba da Bada Tsofaffin Kudi

Sabbin Naira: Yadda ake fama da bankuna kan sabbin kud
Bankuna a Wasu Jihohi Sun Ki Bin Umarnin CBN, Suna Ci Gaba da Ba Tsoffin Kudi | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

Tsoffin kudaden da za su daina amfani sun hada da N200, N500 da N1,000, wadanda aka maye gurbinsu da sabbi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ATM na ci gaba da ba da tsoffin kudade a jihohin Legas, Kano, Nasarawa, Sokoto da sauransu

Jaridar Daily Trust ta ce, wakilanta sun ziyarci injunan cire kudi na ATM a jihohin Legas, Kano, Nasarawa, Sokoto da Adamawa a jiya Alhamis 19 ga watan Janairu.

Sun kuma gano cewa, akwai injunan ATM da yawa da ke ba tsoffin kudi sabanin umarnin da babban bankin Najeriya ya bayar.

A binciken da aka yi a wasu bankunan Kano, babu wanda ke ba sabbin kudi a injunan ATM ya zuwa jiya Alhamis.

Sai dai, bankin Unity a jihar Legas da ke makwabtaka da CBN a jihar na ba da sabbin kudin, hakazalika bankin First Bank da ke kan titi guda da CBN a Legas.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Ya Yi Magana Kan Wa'adin Dena Karbar Tsaffin Naira, Ya Bukaci CBN Ta Kara Wa'adi

A bankin Zenith na titin Zoo road, an ga kusan injunan ATM hudu na ci gaba da ba da tsoffin kudaden.

Za a hukunta bankunan da ke ba da tsoffin kudi a ATM

Kwanturolan yanki na CBN a Kano, Umar Ibrahim Biu ya ce za a hukunta dukkan bankunan da ci gaba da ba da tsoffin kudaden.

A wasu injunan ATM da aka gani a cikin Jami’ar Legas, suna ba da sabbin kudi N1000 da N500, amma wasu suna ci gaba da ba da tsoffin kudaden.

Dillalan shanu sun daina karban tsoffin kudi saboda gudun asara

Dillalan shanu a kasuwar Mararraban Liman Katagum a jihar Bauchi sun bayyanawa CBN cewa, sun daina karbar sabbin kudade saboda gudun asara.

Sun bayyana hakan ne yayin shirin wayar da kan jama’a game da sabbin kudi da kai tsoffi kudaden banki.

Sun kuma koka da cewa, akwai masu sana’ar POS da ‘yan damfara da ke son karbe ‘yan kudaden Fulani da ke shigowa daga kauye.

Kara karanta wannan

Toh fa: CBN ya fadi abin da 'yan Najeriya za su yi idan aka basu tsoffin kudi

Daga karshe sun bukaci a kara wa’adin da aka diba don ba ‘yan kasuwa damar tattara tsoffin kudaden tare da kaiwa banki.

Mahauta na shan fama wajen siyan shanun Fulani

A tattaunawar da wakilin Legit.ng Hausa ya yi da wasu mahauta a kasuwar Waya a jihar Gombe, sun bayyana kokensu game da wa’adin da CBN ya sanya.

A cewar Muhammad Adamu, wani mahauci a kasuwar ya ce:

“Matsalar ita ce, idan kana da tsohon kudi kuma ba Bafulatani a kasuwar kauye ba karya suke ba. Na tura N800,000 ta asusun banki wani wakili na ya siyamin shanu, abin ya gagara, domin tsoffi aka cire, kuma sun ki karba.”

A nasa bangaren, Ishaq cewa ya yi:

“Sabbin ma tsoron karba wasu suke, don haka don Allah ku fadawa Buhari ya kara mana wa’adin, sako daga talakawansa."

A duba wa’adin mayar da tsoffin kudi, Sarkin Musulmi ga CBN

A wani kira da ya yi, Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar ya ce ya kamata babban bankin Najeriya ya duba tare da kara wa’adin mayar da tsoffin kudi.

Kara karanta wannan

Za ku sani: CBN ya fusata, zai yi maganin bakuna yayin da suka ki zuwa daukar sabbin Naira

Ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis 19 ga watan Janairu, inda yace akwai mutane da yawa da ke bukatar a wayar musu da kai game da wannan sabbin kudade.

Sai dai, a nasa bangaren, bankin CBN ya ce babu gudu babu ja da baya, wa’adin dai na nan a ranar 31 ga watan Janairun 2023.

A baya CBN ya ce, duk wanda aka ba tsohon kudi a banki, to kada ya karba saboda wa'adin ya kusa karewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel