Ba Zan Yarda Ba, Mahaifiyar Alkalin Da Aka Bindige Cikin Kotu a Imo Tana Jimami

Ba Zan Yarda Ba, Mahaifiyar Alkalin Da Aka Bindige Cikin Kotu a Imo Tana Jimami

  • Uwar Alkalin da aka kashe kwanakin a cikin kotu ta bayyana bukata guda da take daga wajen gwamnati
  • Iyalan dattijuwar basu fada mata ainihin abinda ya faru ba saboda gudun kada labarin ya illatata
  • Lamarin yan bindiga masu kisa da garkuwa da mutane ya ta'azzara a dukkan sassan Najeriya shida

Mrs Bridget, Mahaifiyar Alkalin da aka kashe a jihar Imo, Nnaemeka Ugboma, ta bukaci gwamnatin jihar ta kama wadanda suka kashe mata 'da a bainar jama'a.

Madam Bridget ta bayyana hakan ne ga manema labarai ranar Asabar, 11 ga wtaan Febrairu, 2023.

Alkali
Ba Zan Yarda Ba, Mahaifiyar Alkalin Da Aka Bindige Cikin Kotu a Imo Tana Jimami
Asali: UGC

A cewarta:

"'Dana mutum ne mai saukin kai. Ba mutum ne mai son yawan magana ba. Bai fada da kowa da zai sa a kashe shi. Har yanzu a rikice nike kan wannan abu."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

"A Cigaba Da Amfani Da Tsaffin Kudi Har Karshen Shekara": Kotun Kolin Najeriya Ta Yanke Hukunci

"'Diyata ce ta bani labarin mutuwarsa. Duk da cewa karya ta min cewa yana fama da rashin lafiya. Yayinda na isa gidansa a Owerri, sai na lura akwai matsala inda na ga dandazon mutane a kofar gidansa."
"Nnaemeka ne 'dana na fari kuma Alkali ne. An fada min wasu yan bindiga ne suka dira kotu a Ejemekwuri suka kasheshi har lahira ba gaira ba dalili."
"Ina kira ga gwamnati da yan sanda sun fito da wadanda suka kashe 'dana kuma su hukuntasu."
"Lauyoyi a jihar nan sun yi matukar damuwa da mutuwar kuma sun yi alkawarin binciko gaskiya."
"Kawai buri ne shine a damke wadanda suka kasheshi."

Yan Bindiga Sun Budewa Tsohon Ministan Buhari Wuta, Mutum Biyu Sun Mutu

A wani labarin daban, Tsohon Ministan Neja Delta kuma dan takaran gwamnan jihar Cross Rivers karkashin jam'iyyar Peoples Redemption Party (PRP), Usani Usani Uguru, ya tsallake rijiya da baya.

Kara karanta wannan

Rudani: Tashin hankali yayin da aka tsinci gawar mata da danta a cikin wani gida a Kano

Wasu yan bindiga sun budewa motarsa wuta a babban titin Calabar-Ikom.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ta ruwaito cewa akalla mutum biyu ne suka rasa rayukansu a harin.

Mr Usani na hanyarsa ta zuwa mahaifarsa ne, garin Nko, dake karamar hukumar Yakurr ta jihar tare da dan takarar mataimakin gwamnan jihar.

Kwamishanan yan sandan jihar, Sule Balarabe, ya tabbatar da labarin harin.

Ya bayyana cewa an kai musu harin ne ranar Juma'a misalin karfe 4 tsakanin karamar hukumar Akamkpa da Biase.

Asali: Legit.ng

Online view pixel