Dakarun Sojoji Sun Kashe Yan Ta'adda Da Dama, Sun Kwato Makamai A Kaduna

Dakarun Sojoji Sun Kashe Yan Ta'adda Da Dama, Sun Kwato Makamai A Kaduna

  • Dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe wasu yan ta'adda hudu tare da kwace babura da kona sansanin yan ta'addan a karamar hukumar Birnin Gwari a Kaduna
  • Laftanant Kwanel Musa Yahaya, mataimakin direktan hulda da jama'a na rundunar sojoji na runduna ta 1 ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a jihar Kaduna
  • Manjo Janar Taoreed Lagbaja, babban kwamandan runduna ta 1, GOC, ya jinjina wa sojojin bisa nasarar da suka yi ya kuma yi kira al'umma su kai rahoton duk wani da aka gani da raunin bindiga

Kaduna - Dakarun sojoji na 1 Division ta Operation Open Whirl Punch sun kashe yan bindiga hudu sun kuma kwato bindigu da wasu makamai a wani samame da suka kai na kimanin awa 48 a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Hankula Sun Tashi Yayin Da Yan Bindiga Suka Kashe Sojoji 4 A Harin Kwanton Bauna A Delta

Mataimakin direktan hulda da jama'a na sojoji, 1 Division, Laftanant Kwanel Musa Yahaya ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Kaduna, rahoton The Punch.

Kaduna Map
Dakarun Sojoji Sun Kashe Yan Ta'adda 4, Sun Kwato Makamai A Kaduna. Hoto: Mobile Punch
Asali: UGC

Yahaya ya bayyana cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ana cigaba da ragargazan yan bindiga, masu garkuwa da yan ta'adda da sauran masu aikata laifuka a arewa maso yamma. Dakarun rundunar ta 1 ta sojojin Najeriya da rundunar sojin sama ta Operation Whirl Punch sun yi wa masu aikata laifuka babban illa.
"A wani hari na kimanin awa 48, dakaruun sun kai hari Manini-Kuriga, Farin Ruwa, Kwanan Yashi, Makera, Dogon Dawa-Maidaro road, dajin Kidanda-Yadi da Sabon Birnin duk a karamar hukumar Birnin Gwari."

Ya bayyana cewa yayin artabun, sojojin sun yi galaba kan masu aikata laifin sun kwato AK-47 daya, harsashi 20 masu tsawon 7.62mm, babura shida, sun kashe hudu sannan wasu sun tsere da raunin bindiga.

Kara karanta wannan

Sauya Naira: Dalilinmu Na Kai Gwamnati, CBN Zuwa Kotu - El Rufai Ya Saki Jawabi

Ya ce:

"Sojojin, a kokarinsu na kawar da bata garin har abada sun kona dukkan sansanin yan ta'addan da kayansu da baburan da aka kwace.
"Babban kwamandan na runduna ta 1, GOC, wanda kuma shine kwamandan Operation Whirl Punch, Manjo Janar Taoreed Lagbaja, ya bayyana gamsuwa da yadda sojojin suka kai harin.
"Lagbaja ya kuma yi kira ga mutanen jihar su sanar da rundunar idan sun ga mutane da raunin bindiga suna neman magani."

Dakarun Sojoji Sun Halaka Yan Ta'adda A Kaduna

A wani rahoton mai kama da wannan dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe yan ta'adda da dama yayin share yankunan Maidaro, Kusharki, Unguwan Madaki, da Kogi Hill a karamar hukumar Birnin Gwari.

Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, kakakin rundunar sojan ne ya sanar da haka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel