An Yiwa Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, Jifar Shaidan a Jiharsa

An Yiwa Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, Jifar Shaidan a Jiharsa

  • Rahotanni sun nuna cewa an tayar da tarzoma a jihar Yobe inda abin ya kai ga cin mutuncin gwamna
  • Gwamna Mai Mala Buni ya halarci taron kamfen Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan
  • Gidan gwamnatin jihar Yobe ta karyata wannan labarin inda tace babu wanda ya jefi Mai Mala

Damaturu - Wasu matasa da ake zargin mabiya Shugaba majalisar dattawa, Ahmed Lawan, ne sun tada tarzoma a wani taro da aka shirya don murnar nasararsa a kotun koli.

Zaku tuna cewa Ahmad Lawan ya samu nasara kan Bashir Machina kan sahihin dan takarar All Progressives Congress (APC) na kujerar Sanatan mazabar Yobe ta Arewa.

Taron ya hargitse ne lokacin da wasu matasa suka fara jifan gwamnan jihar, Mai Mala Buni.

Mai Mala
An Yiwa Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, Jifar Shaidan a Jiharsa
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnoni: Buhari Ya Bada Hakuri Kan Canjin Kudi, Ya Bayyana ‘Yan Takaransa

Premium Times ta ruwaito cewa rikicin ya fara ne lokacin da gwamna Mai Mala Buni ya tashi zai gabatar da jawabinsa.

Fara maganarsa ke da wuya, sai matasa suka fara masa ihun ‘bamayi bamayi bamaso”

Daga bisani matasan suka fara jifansa tare da sauran manyan bakin dake wajen zaman manya.

Haka ya kawo karshen taron inda jami'an tsaro suka fita da gwamnan daga wajen taro.

An tattaro cewa an kaiwa gwamnan wannan hari ne saboda ana ganin cewa shi ya marawa, Bashir Machina baya lokacin da suke ja-in-ja da Ahmaed Lawan kan tikitin.

Matasa Ba Su Farmake Ni Ba a Wajen Kamfen Din APC - Gwamna Buni Ya Magantu

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, Ya Yi watsi da rade-radin da ke yawo cewa wasu fusatattun matasa sun yi masa ruwan duwatsu a wajen wani gangamin siyasa da ya gudana a jihar.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan da sauran mambobin kwamitin yakin neman zaben APC sun halarci gangamin kamfen din.

Kara karanta wannan

Kwamishina Ya Jiƙa Wa APC Aiki, Ya Yi Murabus Daga Muƙaminsa Kwana 10 Gabanin Zaben Gwamnoni

Sai dai an yi ikirarin cewa wasu sun kai wa gwamnan na jihar Yobe hari a yayin taron.

Gwamnan a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Lahadi, 12 ga watan Fabrairu ta hannun kakakinsa, Mamman Mohammed yace:

"Mun karanta cike da damuwa rahotannin kafofin watsa labarai da ke yawo cewa an yi wa wasu masu ruwa da tsakin jam'iyyar ruwan duwatsu a wajen wani gangami a Gashua, jihar Yobe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel