An Samu Jihar APC ta 5 da ta Shigar da Karar Gwamnatin Buhari a Dalilin Canza Kudi

An Samu Jihar APC ta 5 da ta Shigar da Karar Gwamnatin Buhari a Dalilin Canza Kudi

  • Gwamnatin tarayya za tayi shari’a da Gwamnatin Neja a game da batun canjin takardun kudi
  • Kwamishinan harkokin shari’a a Neja, ya ce sun shigar da kararsu wajen Alkalan kotun koli
  • Nasara Danmallam ya ce su na so a tsawaita wa’adin sauya kudin da bankin CBN ya bada

Niger - Gwamnatin jihar Neja ta shigar da karar gwamnatin tarayya a dalilin tsarin da bankin CBN ya fito da shi na canza wasu takardun kudi.

The Cable da ta fitar da rahoton ta bayyana cewa Neja ta zama jiha ta biyar da za tayi shari’a da gwamnatin Muhammadu Buhari a kan tsarin kudin.

Kafin yanzu, gwamnatocin Kaduna, Kogi, Zamfara da kuma Kano duk sun yi karar gwamnatin tarayya, su na so a koma amfani da tsofaffin kudi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamna Ya Fusata, Ya Umarci a Kama Duk Wanda Ya Ƙi Karban Tsoffin Kuɗi

Kwamishinan shari’a kuma babban Lauyan gwamnatin jihar Neja, Nasara Danmallam ya fitar da jawabi cewa sun kai kara gaban koli.

Kara ta je kotun Allah ya isa

Danmallam ya fitar da jawabi, yana cewa kararsu mai lamba SC/CV/210/2023 tana kotun koli tun a ranar Juma’a, su na sa ran a biya masu bukata.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mai girma Kwamishinan ya ce su na rokon babban kotun kasar ta tsawaita wa’adin da bankin CBN ya bada na canza N200, N500 da kuma N1000.

Majalisa
Majalisar magabata Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Lauyoyin Gwamnatin Neja sun sanar da Alkalan kotun cewa karancin sababbin takardun kudin ya jefa al’ummar jihar Neja cikin mawuyacin hali.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, mutanen karkara sun fi shan wahalar tsarin sauya kudin, don haka Kwamishinan ya ce suke neman ceton mutane.

A matsayinsa na Kwamishinan shari’a, Nasara Danmallam ya nuna gwamnatinsu za tayi duk abin da za ta iya domin ganin an raba jama’a da wahala.

Kara karanta wannan

Babu Takardun Buga Sababbin Kudi – Gwamnan CBN Ya Fadi Gaskiyar Halin da Ake Ciki

Kwamishinan yake cewa za su bi duk wata hanya da ba ta sabawa dokar kasa ba. Legit.ng Hausa ba ta da labarin ko an sa lokacin sauraron shari’ar.

Gwamnatin tarayya ta kalubalanci hukuncin farko da aka yi, za a koma kotu a ranar Laraba.

Babu takardun biga Nairori - CBN

A jiya ne rahoto ya zo cewa abin da Gwamnan bankin CBN, Godwin Emefiele ya fada a wajen taron majalisar magabata ya fito fili bayan wasu 'yan sa'o'i.

Babban bankin Najeriya ya karbe tsofaffin N200, N500 da N1000 da ake amfani da su, kuma Emefiele ya nuna yau babu takardun da za a buga sababbin kudi

Asali: Legit.ng

Online view pixel