Kwamishinan Kasafin Kudin Jihar Zamfara Ya Bar APC Ya Koma PDP

Kwamishinan Kasafin Kudin Jihar Zamfara Ya Bar APC Ya Koma PDP

  • Kwamishinan kasafin kudi a Zamfara ya saki tafiyar APC, ya kama jam'iyyar PDP mai adawa gabanin zaben 2023
  • Alhaji Aliyu ya bayyana cewa, ba zai ci gaba da zama a jam'iyyar da gazawarta ta fi nasararta yawa ba
  • Dan takarar gwamnan jihar Zamfara a PDP ya karbi kwamishinan tare da bayyana kwarin gwiwa a zaben bana

Gusau, jihar Zamfara - Sabon rikici na kunno kai a jam'iyyar APC a jihar Zamfara yayin da kwamishinan gwamna Muhammad Bello Matawalle ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP.

Kwamishinan kasafin kudi da tattalin arziki, Alhaji Aliyu Tukur E.S Mafara a wani taron 'yan jarida a Gasau a ranar Juma'a ya ce ya bar jam'iyyar APC tare da komawa PDP; ya marawa dan takarar gwamnan PDP a jihar, Dauda Lawal.

Alhaji Mafara na daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar APC a jihar Zamfara kuma yana daga cikin masu fada a ji a siyasar jihar, Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kano: PDP ta sake rudewa, Atiku ya gaza daura hannu ya fadi dan takarar gwamna

Kwamishinan Zamfara ya koma PDP
Kwamishinan Kasafin Kudin Jihar Zamfara Ya Bar APC Ya Koma PDP, Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Da yake magana bayan ganawa da dan takarar gwamnan na PDP, tsohon kwamishinan ya jaddada cewa, ba zai bari ya ci gaba da zama a inda abu ya ki gaba ya ki baya ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

"Na sanar da gwamnatin jihar, tsohon gwamna da kuma mabiya bayana gabanin sauya sheka daga APC zuwa PDP.
"Ina yin wannan ne saboda mutane na, kuma ina da yakini kan Dr. Dauda Lawal, idan aka ba shi dama ya zama gwamnan Zamfara a zabe mai zuwa, zai shawo kan matsalolin tsaro, ya habaka harkar noma, ya samar da kasuwanni masu kyau ga manoma.
"Saboda haka, na ba da dukkan goyon baya na ga jam'iyyar PDP, kuma ina son yin kira ga magoya bayana a Zamfara da su bi tafiyar Dauda Lawal da PDP a zabe mai zuwa."

Dan takarar gwamnan PDP ya magantu

Kara karanta wannan

Peter Obi Ya Gamu Da Cikas A Yayin Da Jigon Jam'iyyar LP Ya Koma PDP A Ebonyi

A nasa bangaren, dan takarar gwamnan jihar Zamfara na PDP, Dauda Lawal, ya tabbatar da cewa, Zamfara jiha ce ta PDP, inda ya kara da cewa, jam'iyyar za ta sake samun nasarar karbe mulki a zaben 2023, Channels Tv ta ruwaito.

A bangare guda, an yada jita-jitan yadda daya daga ciukin kwamishinonin gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya bar PDP tare da kama APC.

Sai dai, da yake jawabi, ya karyata hakan tare da cewa har yanzu yana tare da gwamnan mai ci a yanzu a jihar ta Sokoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel