An Shiga Rudani, Atiku Ya Gaza Bayyana Dan Takarar da Yake So Ya Gaji Ganduje a Zaben 2023 a PDP

An Shiga Rudani, Atiku Ya Gaza Bayyana Dan Takarar da Yake So Ya Gaji Ganduje a Zaben 2023 a PDP

  • A wani yanayi mai daukar hankali, Atiku ya yi biris da bayyana wanda yake goyon baya ya gaji Ganduje a jihar Kano da ke Arewa maso Yamma
  • Atiku Abubakar ya kai ziyarar kamfen jihar Kano, akwai ayoyin tambaya kan wanda yake tsakanin Muhammad Abacha da Sadiq Wali
  • A bangare guda, Atiku ya bude wata katafariyar makarantar haddar Al-Qur’ani da sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya ya gina

Jihar Kano - Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yi taron kamfen dinsa a jihar Kano, inda ya sake jaddada kudurinsa na bude iyakokin kasa, wanzar da zaman lafiya, inganta noma da masana’antu da dai sauransu.

Sai dai, taron ya zo da wani salo yayin da Atiku ya kame baki, ya gaza bayyana dan takarar gwamnan Kano a PDP da yake goyon baya a zaben 2023 mai zuwa.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: An gina makarantar haddar Al-Qur'ani cikin wata 6 a Kano, Atiku ya kaddamar da ita

Watakila wannan ya faru ne sakamakon samun sinki biyu na ‘yan takarar da suke ci gaba da kai ruwa rana kan tikitin na takarar gwamna na PDP a jihar ta Kano, Naija News ta tattaro.

Atiku ya gaza zaben sahihin dan takarar gwamnan Kano
An Shiga Rudani, Atiku Ya Gaza Bayyana Dan Takarar da Yake So Ya Gaji Ganduje a Zaben 2023 a PDP | Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

A al’adar kamfen na Najeriya, dan takarar shugaban kasa kan daga hannu dan takarar gwamna tare da bashi tutar jam’iyya a lokacin da ya zo kamfen jiharsa, amma ba a yi hakan ba a PDP a jihar Kano a taron bana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rikicin cikin gida a PDP a jihar Kano

Idan baku manta ba, rikicin cikin gida PDP ke fuskanta a Kano yana faruwa ne tsakani ‘yan takarar gwamna biyu; Muhammad Abacha da Sadiq Wali.

A hannun hukumar zabe ta INEC, sunan Wali ne a rubuce, yayin da kotu kuma ta bayyana amincewarta da sahihancin Muhammad Abacha.

Kara karanta wannan

2023: APC na kitsa yadda za su sa kiristoci su tsane ni, Atiku ya tono sirrin 'yan APC

Daily Trust ta ruwaito cewa, wakilinta ya ga ‘yan takarar gwamnan PDP biyu a taron gangamin tare da Atiku Abubakar da kuma abokin takararsa, gwamna Okowa na Delta.

Dalilin da yasa Atiku bai nuna wanda yake goyon baya ba

Atiku bai ambaci sunayensu ba, bai kuma daga hannun daya daga cikinsu ba a matsayin zabinsa na wanda zai yi takara a Kano.

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce, jam’iyyar PDP da dan takararta na shugaban kasa na yin kaffa-kaffa da abin da ka iya biyowa baya ne gabanin hukuncin da kotun koli za ta yanke kan lamarin gobe Juma’a 10 ga watan Faburairu.

A ziyarar da Atiku ya kai Kano ne ya bude wata makarantar haddar Al-Qur’ani da Shekarau ya gina a garinsu, ya saka mata sunan kakansa; Gwani Muhammad Dan Gunduwawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel