Peter Obi Ya Gamu Da Cikas A Yayin Da Jigon Jam'iyyar LP Ya Koma PDP A Ebonyi

Peter Obi Ya Gamu Da Cikas A Yayin Da Jigon Jam'iyyar LP Ya Koma PDP A Ebonyi

  • Injiniya Henry Ude, jigon dan siyasa a jihar Ebonyi ya fita daga jam'iyyar Labour, LP, ya koma PDP
  • Dan takarar sanatan na mazabar Ebonyi South a karkashin jam'iyyar LP ya ce kishin jiharsa da mutane yasa ya koma PDP
  • Ya yi kira ga sauran al'ummar jihar ta Ebonyi su mara masa baya a yayin da ya ke kokarin bada gudunmawarsa na yanta yan jihar

Jihar Ebonyi - Fitaccen dan siyasa kuma daya cikin wadanda aka kafa jihar Ebonyi da su, Injiniya Henry Ude, da aka fi sani da Ajim Best, ya fita daga jam'iyyar Labour ya koma PDP.

A cewarsa, ya gamsu cewa jam'iyyar PDP za ta iya dawo da zaman lafiya, tsaro da yanci ga mutanen jihar, rahoton Nigerian Tribune.

LP da PDP
Peter Obi Ya Gamu Da Cikas A Yayin Da Jigon Jam'iyyar LP Ya Koma PDP A Ebonyi. Hoto: Nigerian Tribune
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Shiga Tasku, Wani Kusa a APC Ya Fice Daga Jam'iyyar Kwana 17 Kafin Zaben 2023

Cif Ude wanda shine dan takarar sanata na mazabar Ebonyi South a LP, ya sanar da komawarsa PDP ne yayin zantawa da manema labarai a Abakaliki, rahoton The Punch.

Ya ce ya yanke shawarar komawa PDP don taimakawa wurin cika burinsa a matsayin daya cikin iyayen jihar na bada gudumawa don ceto jihar daga mawuyacin halin da ta shiga.

Kalamansa:

"Yanzu na dawo PDP don hada hannu da sauran masu kishi da ke neman ganin mutane sun samu yancin zirga-zirga, zumunci da samun cigaba."

Ya yi kira ga mutanen jihar su hada hannu da sabuwar tafiyar siyasa karkashin jagorancin dan takarar gwamna na PDP, Dr Ifeanyi Chukwuma Odii don kwato mulki daga hannun APC.

Ya cigaba da cewa:

"Ina tabbatar wa mutanen Ebonyi cewa abin zai yiwu, kuma PDP za ta iya kwato nasararta da aka sace domin dora jihar kan turbar cigaba ta hanyar samar da gwamnati mai kyau da za ta kula da bukatun al'umma."

Kara karanta wannan

2023: APC na kitsa yadda za su sa kiristoci su tsane ni, Atiku ya tono sirrin 'yan APC

Sirri na a rayuwa shine rashin tsaro, Ude

Cif Ude ya jadadda cewa 'sirrin rayuwa shine, 'ka zama mara tsoro.

Idan an tura ka, ka cigaba da tafiya, kada ka dena tafiya. Dai taimakon Ubangiji, za mu yanta jihar Ebonyi.

Idan za a iya tunawa Ude na cikin iyayen jihar Ebonyi karkashin jam'iyyar PDP kuma ya yi fice wurin daukan nauyin talla yayin gwagwarmayar neman kafa jihar Ekiti.

Jigon jam'iyyar APC a Ondo ya koma LP

A bangare guda, Stephen Adeyeri, dan takarar da ya nemi tikitin majalisar tarayya a karkashin APC a Ondo ya koma jam'iyyar Labour.

Asali: Legit.ng

Online view pixel