Soja Ya Caka Wa Mai Karbar Haraji A Kasuwa Wuka Ya Kashe Shi Saboda N100

Soja Ya Caka Wa Mai Karbar Haraji A Kasuwa Wuka Ya Kashe Shi Saboda N100

  • Wani soja ya yi sanadin rasuwar wani mai karbar haraji hanun yan kasuwa ta hanyar daba masa wuka a unguwar Oshodi, Legas
  • Lamarin ya faru ne a lokacin da dan kasuwar ke kokarin karbar kudin tikitin haraji daga hannun wata yar kasuwa
  • Matar ta yi gardamar biyan kudin hakan ya janyo cacar baki, shi kuma sojan ya nemi a hana karbar kudin daga hannun matar har ya caka wa mai karbar wuka

Legas - Wani soja da ba a riga an bayyana sunansa ba ya daba wa mai karbar haraji, Ibrahimi Ikudaisi, wanda aka fi sani da Guardian, wuka ya kashe shi saboda tikitin N100 a Oshodi, Legas.

Punch Metro ta tattaro cewa Ikudaisi yana ziyarar shaguna ne don karbar harajin N100 daga wurin yan kasuwa a Oshodi amma wata yar kasuwa ta ki biya.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Na San Yadda Zan Yadda Zan Gyara Tattalin Arzikin Najeriya, Bola Tinubu

Jihar Legas
Soja Ya Caka Wa Mai Karbar Haraji A Kasuwa Wuka Ya Kashe Shi Saboda N100. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rashin biyan ya janyo cacar baki tsakanin Ikudaisi da yar kasuwar shi kuma sojan ya sa baki don hana matar biyan kudin harajin.

An rahoto cewa cacar bakin ya yi zafi har ta kai sojan ya ciro wuka ya daba wa Ikudaisi a kirjinsa.

Wani shaidan gani da ido ya magantu

Wani wanda abin ya faru a idonsam Adenike Ajayi ya shaida wa wakilin Punch cewa wukar da sojan ya caka wa Ikudaisi ta sa ya fadi kasa hakan yasa sojan ya tsere.

Ajayi ya ce:

"Ikudaisi sanannen mutum ne a yankin nan na Oshodi. Kowa ya san shi da lakabin 'Guardian'. Yana daya cikin wadanda ke karbar harajin tikiti daga wurin mu masu tireda.
"Jiya (Talata) ya taho misalin karfe 11 na safe kuma duk mun biya kudin mu lokacin da ya fara cacar baki da wata mata wacce bata biya ba.

Kara karanta wannan

"Nima Ina Ji A Jiki Na", Minista Mai Karfi A Gwamnatin Buhari Ya Ce Shi Kansa Ba Shi Da Sabbin Takardun Naira

"A yayin da suke jayayya, wani soja ya taho ya nemi hana matar biyan harajin na N100. Nan take, abu ya rikice har sojan ya fito da wukarsa ya daba wa Ikudaisi a kirji."

Ajayi ya ce sojan ya tsere ya tafi barikin su da ke Charity, inda wasu sojojin suka cece shi, ya kara da cewa Ikudaisi ya mutu saboda raunin da ya samu daga harin.

Tiredan ya cigaba da cewa:

"An birne shi yau da safe a gidansu da ke Legas da safe. Sojoji sun taho nan da safe sun fada mana an kama sojan amma ba mu yarda ba domin babu wanda ya ga lokacin da aka kama shi."

Martanin yan sanda

Kakakin yan sandan Legas, SP Benjamin Hundeyin da aka tuntube shi ya ce:

"Ban samu labarin afkuwar lamarin ba; zan tuntube ka da zarar na samu bayani kan lamarin."

A bangarensa, mataimakin direktan watsa labaran sojoji na 81 Division, Olabisi Ayeni, ya ce rundunar ta san da faruwar abin kuma tana bincike don gano gaskiya.

Kara karanta wannan

Buhari ka farka, ka kawo karshen karancin Naira, Sanata ya koka, ya roki Buhari

Wani mutum ya halaka dan uwansa saboda N1,000 a Legas

A wani labari mai kama da wannan, wani Ibrahim Dauda, ya halaka dan uwansa mai suna Tunde sakamakon dambe da suka yi kan N1000.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164