Kotun Koli Ta Tabbatar da Emenike a Matsayin Dan Takarar Gwamnan Jam’iyyar APC a Abia

Kotun Koli Ta Tabbatar da Emenike a Matsayin Dan Takarar Gwamnan Jam’iyyar APC a Abia

  • Ikechi Emenike ne dan takarar da kotun koli ta amince ya yi takarar gwamna a jam'iyyar APC a jihar Abia
  • Wannan na zuwa ne bayan da kotun daukaka kara ta bashi gaskiya a baya, amma aka daga karar saboda dalilai
  • A makon nan ne Uba Sani ya zama cikakke kuma sahihin dan takarar APC a matakin gwamna a jihar Kaduna bayan hukuncin kotun koli

FCT, Abuja - Kotun koli ta tabbatar da Ikechi Eminike a matsayin sahihin dan takarar gwamnan jihar Abia a jam'iyyar APC a zaben 2023 mai zuwa, TheCable ta ruwaito.

Wannan na zuwa ne a cikin hukuncin da alkalai biyar na kotun karkashin jagorancn Tijani Abubakar suka yanke a ranar Alhamis 9 ga watan Faburairu.

Idan baku manta ba, an daukaka karar zuwa kotun kolin ne bayan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a watan Disamban bara.

Kara karanta wannan

Abubakar Malami da Emefiele Duk Makiya Al'umma Ne: Mai Magana Da Yawun Tinubu

Emenike ya zama sahihin dan takarar APC a Abia
Kotun Koli Ta Tabbatar da Emenike a Matsayin Dan Takarar Gwamnan Jam’iyyar APC a Abia | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Yadda batun ya faro tun farko

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farkon zancen, a ranar 11 ga watan Nuwamba, mai shari’a Binta Nyako ta babban kotun tarayya ta kori Emenike tare da tabbatar da Ogah a matsayin sahihin dan takarar gwamnan APC a Abia.

Jam’iyyar APC da Emenike suka kai maganar gaban kotun daukaka kara domin kalulantar hukuncin Nyako.

Dan Eke, wani dan takarar na daban shima ya daukaka kara kan hukuncin da ke tabbatar da Ogah a matsayin sahihin dan takarar APC.

A watan Disamban bara, kotun daukaka kara mai zama a Abuja ta tabbatar Emenike a matsayin dan takarar APC, Tribune Online ta ruwaito.

A wannan karon ma ya yi nasara bayan da aka daukaka kara zuwa kotun koli, inda aka ce shine sahihin dan takarar APC.

Kotun koli ta yi hukunce-hukunce da yawa a cikin wannan makon.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Hukumar EFCC ta kulle Sanatan APC Gidan Yari Bisa BAdakalar N805m

An tabbatar da Uba Sani a matsayin dan takarar gwamnan APC a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji yadda kotun koli ta ba Sanata Uba Sani gaskiya, shine sahihin dan takarar gwamnan APC a jihar Kaduna.

Wannan na zuwa bayan hukunce-hukunce biyu na babbar kotu da ta daukaka kara a lokuta mabambanta a shekarar da ta gabata.

Dama El-Rufai ya zabi Uba Sani a matsayin wanda yake so ya gaje shi a zaben gwamna da za a yi a Najeriya a ranar 11 ga watan Maris na shekarar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel