Kotun Koli Ta Tabbatar da Zabin El-Rufai, Sani Uba a Matsayin Dan Takarar Gwamnan APC Na Kaduna

Kotun Koli Ta Tabbatar da Zabin El-Rufai, Sani Uba a Matsayin Dan Takarar Gwamnan APC Na Kaduna

  • Sanata Uba Sani ne zai rike turar jam'iyyar APC a zaben gwamnan jihar Kaduna da za a yi nan ba da jimawa ba
  • Sanatan ya tsallake kotu uku, inda aka bashi gaskiya a takarar da ya tsaya tare da abokin hamayyarsa na APC, Sani Sha'aban
  • Yanzu dai shirin gwabzawa a zaben 11 ga watan Maris ne ya saurawa dan takarar bayan wanke komai daga kotu

Kotun koli a Najeriya ta yi watsi da daukaka kara biyu da aka shigar kan hukumar zabe ta INEC, jam’iyyar APC da dan takarar gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani ta Sani Mahmoud Sha’aban.

Lauyan APC, wanda kuma shine tsohon shugaban kungiyar lauyoyi ta NBA reshen jihar Kaduna, Sule Shu’aibu Esq. ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kaduna.

Uba sani ne zai rike tutar APC a Kaduna
Kotun Koli Ta Tabbatar da Zabin El-Rufai, Sani Uba a Matsayin Dan Takarar Gwamnan APC Na Kaduna | Hoto: Senator Uba Sani
Asali: Twitter

Legit.ng ta samo cewa, lauyan ya ce:

Kara karanta wannan

2023: APC na kitsa yadda za su sa kiristoci su tsane ni, Atiku ya tono sirrin 'yan APC

“Daga karshe, daukaka kara biyu da Sani Mahmoud Sha’aban ya shigar kan APC, dan takarar gwamnanta, Uba sa da INEC an yi watsi ita da safen nan, hakan ya kawo karshen kitmurmurar da ta faro a kotun tarayya da ke Kaduna, inda aka nemo korar dan takarar gwamnan APC daga takara a zabe mai zuwa.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Damar sanata Sani a zaben gwamnan da ke tafe

Wannan hukuncin na kotun koli na nufin, sanata Sani ne zai rike tutar jam'iyyar APC a zaben gwamnan da za gudanar a watan gobe.

Sanatan dai shine ke burin gaje kujerar gwamnan jihar mai ci a yanzu, Malam Nasiru El-Rufai, wanda kuma dama gwamnan shi ya fi so don gaje shi a zaben bana.

Idan baku manta ba, an kai ruwa rana tsakanin 'yan takarar guda biyu a kotun tarayya, daukaka kara da yanzu a kotun koli, zance ya kare.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Zanga-Zanga Ya Barke a Abeokuta kan karancin Naira da tsadar mai, an kai hari Banki

Kalubalen da za a samu a zaben 2023, ini tsohon shugaban INEC Attahiru Jega

A wan labarin, yayin da zabe ke karatowa, tsohon shugaban INEC ya bayyana abin da yake hangowa da a lokacin da za a yi zaben.

Jega ya bayyana cewa, kalubalen zaben 2023 ba komai bane face masu kada kuri'un da kansu da kuma 'yan siyasar da basu tuba da zamba ba.

Ya ce, babu abin da ya sauya daga halin 'yan siyasar Najeriya tun 1999 zuwa zaben wannan shekarar da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel