Wike ya yaba da Hukuncin Kotun koli, Yace Ribas Zata Shiga Shari'a da FG

Wike ya yaba da Hukuncin Kotun koli, Yace Ribas Zata Shiga Shari'a da FG

  • Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya nuna farin cikinsa da hukuncin Kotun koli kan wa'adin da CBN ya gindaya
  • Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin Ribas zata shiga karar da aka maka gwamnatin tarayya kan sabbin naira
  • A ɗazu asusun ba da lamuni na duniya ya shawarci babban bankin Najeriya ya kara wa'adin amfani da tsohon kuɗi

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yaba wa Kotun Koli bisa ceto 'yan Najeriya da Demokaradiyya ta hanyar hana CBN aiwatar da tsarinsa, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Wike ya nuna jin dadinsa bisa hukuncin da Kotun koli ta yanke na hana babban bankin Najeriya haramta amfani da tsoffin takardun N200, N500 da N1000 ranar 10 ga watan Fabrairu.

Wike.
Wike ya yaba da Hukuncin Kotun koli, Yace Ribas Zata Shiga Shari'a da FG Hoto: Nyesom Wike
Asali: Facebook

Gwamnan ya bayyana haka ne a wurin gangamin yakin neman zaɓen jam'iyar PDP reshen jihar Ribas wanda ya gudana a ƙaramar hukumar Abua/Odual.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Kasa ta birkice, 'yan Najeriya sun fara zanga a hedkwatar CBN bayan hukuncin kotu

Yayin ralin kamfen na yau Laraba, Wike ya roki ɗaukacin al'ummar Ribas su killace katunan zaɓensu kana su jefa wa 'yan takarar PDP kuri'unsu a matakin jiha.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wike ya yaba wa Kaduna, Zamfara da Kogi

Sai dai da yake tsokaci kan hukuncin Kotun ƙoli, gwamnan ya yaba wa gwamnatocin johohi uku da suka haɗa guiwa suka shigar da ƙarar FG.

Jaridar Punch ta rahoto cewa jihohin da suka haɗu suka shigar karar gaban Kotun Koli su ne Kaduna, Kogi da kuma Zamfara.

Bugu da ƙari, Nyesom Wike ya bayyana cewa gwamnatin jihar Ribas zata shiga shari'ar wacce aka kai ƙarar gwamnatin tarayya. Ya ƙara da cewa PDP a Ribas ba ta goyon bayan tsarin CBN.

Haka zalika Gwamna Wike ya ce Kotun ƙoli ta hanyar wannan hukuncin da ta yanke ta ƙara tabbatar da cewa shari'a ce kaɗai gatan talaka.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Buhari na ganawar sirri da gwamnan CBN bayan hukuncin kotun koli kan batun kudi

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa matakin CBN na haramta amfani da tsofaffin takardun kuɗi a ranar 10 ga watan Fabrairu, ya fusata da yawan 'yan Najeriya duba da karancin sabbin a hannun mutane.

A wani labarin kuma mun tattaro muku muhimman bayanai game da wa'adin daina amfani da tsoffin kuɗi wanda CBN ya gindaya

Idan baku manta ba gwamnan babban bankin kasa ya ce bankuna zasu karbi tsohon naira ko da wa'adin da aka sanya ya wuce.

Tun da fari CBN da zabi ranar 31 ga watan Janairu a msatayin wa'adin daina amfani da kuɗin daga baya kuma ya ƙara kwana 10 bayan zama da Buhari a Daura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel