Bayani Dalla-Dalla: Shin Yaushe Ne Ainihin Wa'adin Musayar Kudi 10 ko 17 Ga Wata?

Bayani Dalla-Dalla: Shin Yaushe Ne Ainihin Wa'adin Musayar Kudi 10 ko 17 Ga Wata?

Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya ce CBN zai karɓi tsaffin takardun kuɗi har bayan cikar wa'adin da ya gindaya 10 ga watan Fabrairu, 2023.

A ranar Talata, yayin da yake karin haske a gaban kwamitin wucin gadi na majalisar wakilan tarayya, Gwamnan yace kundin dokokin CBN ya tanadi dokar cigaba da karban kuɗin bayan cikar wa'adi.

Sabbi da tsaffin kuɗi.
Bayani Dalla-Dalla: Shin Yaushe Ne Ainihin Wa'adin Musayar Kudi 10 ko 17 Ga Wata? Hoto: cbn
Asali: UGC

Tsakanin 10 da 17, yaushe ne wa'adin CBN?

Idan baku manta ba, Legit.ng Hausa ta kawo maku rahoton cewa Mista Emefiele, ya sanar da kara wa'adin musanya tsohon kuɗi da sabo da kwana 10.

Sakamakon haka wa'adin daina amfani da tsoffin takardun kuɗin naira da musanya ya tashi daga 31 ga watan Janairu, zuwa 10 ga watan Maris, 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Sabon Tsari: CBN Ya Ƙara Shigo da Abu 2 da Zasu Rage Wa 'Yan Arewa Wahalar Neman Sabbin Kuɗi

Bugu da ƙari, Godwin Emefiele, ya sanar da ƙarin 'Takaitaccen lokacin alheri' na kwana 7 wanda zai ba 'yan Najeriya damar maida tsoffin ƙuɗi zuwa CBN kai tsaye bayan wa'adi ya cika.

Gwamnan CBN ya yi bayanin cewa mutane zasu iya amfani da wannan dama ta maida tsaffin kuɗi zuwa CBN kai tsaye daga 10-17 ga watan Fabrairu, 2023.

Wane bankuna zasu karɓi tsoffin kuɗi bayan wa'adi ya cika?

A jawabinsa yayin da ya amsa gayyatar majalisar wakilai, Emefiele, ya bayyana cewa ya zama tilas kan baki ɗaya bankunan kasuwanci su karbi tsohon kuɗi ko da kuwa wa'adi ya cika.

Gwamnan CBN da Buhari.
Bayani Dalla-Dalla: Shin Yaushe Ne Ainihin Wa'adin Musayar Kudi 10 ko 17 Ga Wata? Hoto: Buhari Sallau
Asali: UGC

Gwamnan CBN ɗin ya ce ya amince da tanadin doka a sashi na 20 (3) wanda ya umarci bankunan kasuwanci su ci gaba da amsar tsaffin takardun kuɗi bayan lokacin da aka ɗiba ya wuce.

Legit.ng Hausa ta binciko dokar sashi na 20 (3) a kundin dokokin CBN, wanda ya tanadi:

Kara karanta wannan

Labari Mai Dadi: CBN Ya Gano Masu Ɓoye Miliyoyin Sabbin Kudi, Ya Fadi Abinda Ya Dace Mutane Su Yi

"Ba tare da la'akari da karamin sashi na 1 da 2 ba, banki na da iko, bisa umarnin shugaban ƙasa, ya cigaba da karban tsohon kuɗin ko da kuwa sun rasa halascin doka, amma bisa sashi na 22, banki zai iya dawo da su idan da bukatar haka."

Gwamnan CBN ya jaddada cewa ya wajaba kan bankuna kasuwanci su cigaba da karban tsohon takardun kuɗin har bayan karewar wa'adin 10 ga watan Fabrairu, 2023.

Babu wanda zai yi asara - Emefiele

Baya ga haka, Babban bankin Najeriya ya tabbatar da cewa babu wani ɗan Najeriya ba zai yi asarar tsohon kuɗin da ya mallaka sakamakon sabon tsarin da aka bullo da shi.

CBN ya yi bayanin cewa ya dauki matakai daban-daban domin tabbatar da sabbin takardun kuɗin sun isa hannun jama'a kamar yadda Premium Times ta ruwaio.

Tsarin sauya takardun naira N200, N300, N500 ya jefa 'yan Najeriya da dama cikin ƙangin wahala, da yawan mutane sun maida tsohon kuɗi bankuna gudun asara amma sabbin sun yi wahala.

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare: Gwamnan CBN Ya Tona Asiri Kan Sabbin Kudi, Ya Faɗi Babban Laifin Bankuna

Lamarin dai ya haddasa cece-kuce a faɗin ƙasar nan yayin da bankuna da CBN ke dora wa juna laifi. Wasu 'yan siyasa sun yi ikirarin an kirkiri tsarin ne domin a yake su.

CBN Ya Boye Sabbin Kudi Ya Bar Mutane Cikin Wahala, Badaru

A wani labarin gwamna Badaru na jihar Jigawa ya nuna takaicinsa kan yadda CBN ke wahal da al'umma wajen neman takardun kuɗi

Gwamnan ya nuna damuwarsa game da karancin sabbin kuɗin ta bakin kwamishinan kudi da bunkasa tattalin arziki na jihar, Babangida Umar Gantsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel