Bayan Hukuncin Tsawaita Wa’adin Kashe Tsoffin Kudi, ’Yan Najeriya Sun Fito Zanga-Zanga

Bayan Hukuncin Tsawaita Wa’adin Kashe Tsoffin Kudi, ’Yan Najeriya Sun Fito Zanga-Zanga

  • Wasu 'yan Najeriya sun bayyana damuwarsu da yadda kotu ta kawo batun tsawaita wa'adin kashe tsoffin Naira
  • A baya CBN ya ce, daga ranar 10 ga watan Faburairu, tsoffin N200, N500 da N1000 sun daina aiki
  • Masu zanga-zanga sun nemi a dakatar da hukuncin kotu, 10 ga watan nan ya zama karshen tsoffin Naira

FCT, Abuja - Masu zanga-zanga sun mamaye hedkwatar CBN da ofishin atoni-janar na kasa kan batun hukuncin kotun koli game da wa’adin daina amfani da tsoffin Naira, TheCable ta ruwaito.

Idan baku manta ba, kotu koli a ranar Laraba 8 Faburairu, 2023 ta yanke hukuncin yin watsi da wa’adin da CBN ya diba na daina amfani da tsoffin Naira nan da 10 ga watan Faburairu.

Gwamnonin Arewa na APC uku; El-Rufai, Yahaya Bello da Matawalle ne suka shigar da karar neman yin watsi da wa’adin a makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Buhari na ganawar sirri da gwamnan CBN bayan hukuncin kotun koli kan batun kudi

Yadda aka yi zanga-zangar nuna kin jinin hukuncin kotun koli
Bayan Hukuncin Tsawaita Wa’adin Kashe Tsoffin Kudi, ’Yan Najeriya Sun Fito Zanga-Zanga | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Yadda aka zo zanga-zanga a yau Laraba

A yake jawabi ga manema labarai, Obed Agu, daga daya shugabannin masu zanga-zangar ya ce ya kamata Buhari ya ba da umarnin iko don tabbatar da wa’adin 10 ga watan Faburairu don daina amfani da tsoffin kudi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Agu ya kuma bayyana cewa, hukuncin kotun bai yi daidai da doka ba, don haka ta yin haka kotun ya ba ‘yan siyasa damar siyan kuri’u a zaben 2023.

A cewarsa:

“Muna kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ba da umarnin iko don tabbatar da wa’adin 10 ga watan Faburairu da kma hana tsawaita shi.
“Kotun kolin na son taimakawa gurbatattun ‘yan siyasa ne wajen siyan kuri’u.”

A yi watsi da hukuncin kotun koli

Hakazalika, ya yi kira ga alkalin alkalan Najeriya da ya yi watsi da hukuncin kotun bisa bin muradin ‘yan kasa, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: APC na kitsa yadda za su sa kiristoci su tsane ni, Atiku ya tono sirrin 'yan APC

Ya kara da cewa:

“Mun sha wahala matuka a hannun kotun koli wajen kokarin kawo tsaiko ga ingantaccen zabe. Kotun koli ne ya hana amfani da injin karanta katin zabe wanda ke taimakawa wajen hana murdiya a sakamakon zabe.

Kunji cewa, bayan hukuncin ne gwamnan CBN ya shiga wata ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa ta Aso Rock.

Asali: Legit.ng

Online view pixel