Shugaban INEC Na Sa Labule Da Majalisar Zartaswa Ta Kasa Game Da Zaben 2023

Shugaban INEC Na Sa Labule Da Majalisar Zartaswa Ta Kasa Game Da Zaben 2023

  • Shugaban hukumar zabe ta kasa, Farfesa Mahood Yakubu, ya bayyana a gaban majalisar zartaswa ta kasa a yau Laraba, 8 ga watan Fabrairu
  • Yakubu zai sanar da shugaba Muhammadu Buhari da mambobin majalisar shirye-shiryensu kan babban zaben kasar mai zuwa nan da kwanaki 17
  • A ranar 25 ga watan Fabrairu ne za gudanar da zaben shugaban kasa a fadin kasar domin fitar da magajin Shugaba Buhari

Abuja - Shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahood Yakubu, na cikin wata ganawa da majalisar zartaswa ta kasa wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ke jagoranta, jaridar The Nation ta rahoto.

Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, ne ya sanar da hakan jim kadan bayan Buhari ya isa zauren majalisar kafin a shiga taron a tsakanaki.

Yayin da babban zaben kasar ya rage saura kwanaki 17, ana sanya ran Yakubu zai yi wa majalisar zartarwar bayani kan shirinsu ga zaben da za a yi a fadin kasar, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Karancin Naira Da fetur: Shugaban INEC Ya Fadi Matsayarsa Game Da Yiwuwar Samun Matsala a Zaben Bana

Taron majalisar zartaswa
Shugaban INEC Na Sa Labule Da Majalisar Zartaswa Ta Kasa Game Da Zaben 2023 Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Har ila yau, ana sanya ran Sufeto Janar na yan sanda, Usman Alkali Baba zai yi wa majalisar jawabi, amma dai har yanzu bai isa zauren ba yayin da aka fara ganawar da misalin 9:58 na safiyar yau Laraba, 8 ga watan Fabrairu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kafin Yakubu ya yi jawabi ga mambobin majalisar, an yi shiru na tsawon minti daya don karrama Air Commodore Dan Suleiman (retd), tsohon ministan ayyuka na musamman a karkashin mulkin Janar Yakubu Gowon.

Yakubu ya gana da gwamnan CBN da Monguno

Idan za ku tuna, Yakubu ya gana da babban mai ba kasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno da gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele a ranar Talata don tattauna karan tsayen da sabon manufar CBN ya kawo wa shirye-shiryen zaben.

Shugaban na INEC ya samu tabbaci daga Monguno na samar da cikakken tsaro yayin da gwamnan CBN ma ya ce zai samar da duk tsabar kudin da hukumar za ta bukata da harkokinta.

Kara karanta wannan

Matsaloli Sun Dabaibaye Kasa: Shugaba Buhari Zai Jagoranci Zaman Majalisar Magabatan Najeriya Yau Juma'a

Ku yi waje da gwamnatin APC, Saraki ga yan Najeriya

A wani labari na daban, shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya bukaci yan Najeriya da su yi waje da APC a zabe mai zuwa saboda kangin wahalar da ta jefa su tsawon shekaru takwas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel