Hukumar ICPC Ta Bankado Sabbin N258m da Aka Boye a Ma’ajiyar Banki a Abuja, Ta Kama Manajoji

Hukumar ICPC Ta Bankado Sabbin N258m da Aka Boye a Ma’ajiyar Banki a Abuja, Ta Kama Manajoji

  • Wani banki a Najeriya ya jawo wa kansa tasku yayin da jami’an hukumar ICPC suka dura don yin kame kwatsam a Abuja
  • An gano kunshin kudade masu yawa sabbi da CBN ya bayar a raba wa ‘yan Najeriya a lokacin karancin sabbin kudi a kasar
  • An kama manajojin bankuna bisa zarginsu da hana ‘yan Najeriya sabbin kudade duk da kuwa akwai kudaden a kasa

FCT, Abuja - Hukumar dakile cin hanci da rashawa ta ICPC ta bankado wasu makudan kudade N258m a wani dakin ajiya na bakin Najeriya yayin da ake fama da karancin sabbin Naira.

Azuka Oguga, mai magana da yawun hukumar ce ta bayyana hakan, inda tace an gano kudaden ne dakin ajiyar kudi na hedkwatar bankin Sterling da ke babban birnin tarayya Abuja.

Idan baku manta ba, tun bayan sauya fasalin N200, N500 da N1000 da kawo sabbi ake fama da karancin kudi a kasar nan, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

A ina kika samo: Kowa girgiza, wata mata ta samo damin kudi, tana siyar da N50k a farashin N60k

Jami'an ICPC sun kama masu boye kudi a banki
Hukumar ICPC Ta Bankado Sabbin N258m da Aka Boye a Ma’ajiyar Banki a Abuja, Ta Kama Manajoji | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A cewar mai magana da yawun ICPC:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Jami’an ICPC sun bankado kudadeNaira miliyan dari biyu da hamsin da takwas (N258m) a makare a ma’ajiyar hedkwatar bankin Sterling da ke Abuja.”

CBN ya ba da kudi a raba, banki ya boye

A cewarta, bincike ya nuna cewa, babban bankin Najeriya (CBN) ya ba Sterling kudaden domin rabawa ‘yan Najeriya, amma bankin ya gaza yin hakan, rahoton Punch.

Ta kara da cewa:

“Daga baya jami’ai sun gano cewa N5m kacal aka rabawa kowane bankin reshe a fadin kasar.”
“An kama manajan shiyya da na aiki amma daga baya aka ba da belinsu kan tsarin aiki inda bincike zai ci gaba.”

A bangare guda, ya hukumar ta kama manajan bankin Keystone da ke Mararaba a jihar Nasarawa bisa laifin kuntatawa kwastomomi game da sabbin Naira.

Kara karanta wannan

Toh fah: Makiyin Najeriya ne zai kawo batun sauyin kudi yanzu, inji dan takarar shugaban kasa

Wata mata ta sami sabbin kudi, tana siyarwa a bakin titi

A wani labarin kuma, an ga bidiyon wata mata da ke siyar da sabbin Naira a bakin titi, mutane sun zagayeta suna saye a farashi mai ban mamaki.

An ce tana karbar N60,000 ga duk wanda ke son N50,000, duk da haka mutane na sayen kudin don biyan bukatunsu.

'Yan Najeriya na ci gaba da kuka da rokon gwamnati kan ta samo mafita ga matsalar karancin sabbin kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel