Kiyayya Ga Kasa Ne Yasa Aka Sauya Fasalin Naira, Inji Dan Takarar Shugaban Kasa

Kiyayya Ga Kasa Ne Yasa Aka Sauya Fasalin Naira, Inji Dan Takarar Shugaban Kasa

  • Mr Yabagi Sani, dan takarar shugaban kasa a Najeriya ya bayyana rikicin da ke tattare da sauyin fasalin Naira da CBN ya yi
  • Ya ce wannan ba komai bane face kiyayya ga Najeriya, kuma tabbas an kuntatawa ‘yan Najeriya da ke fama da rashin tsaro da fatara
  • Peter Obi kuwa, ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi hakuri, kana su yiwa Buhari da CBN uzuri game da batun sauya fasalin kudi

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar ADP, Mr Yabagi Sani ya caccaki yadda Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sauya fasalin Naira.

Bayan kirkirar sabbin N200, N500 da N1000 da CBN ya yi, ‘yan Najeriya na ci gaba da fuskantar karancin kudi a dukkan yankunan kasar.

Da yake magana a wata tattaunawa da Channels Tv, Sani ya ce, sabbin ka’idojin kudi na CBN ba komai bane face wani shiri na kawo tsaiko ga siyasa da dimokradiyyar kasar.

Kara karanta wannan

Masu Tunanin Akwai Wani Sabani Tsakanina da Buhari Za Su Ji Kunya Inji Tinubu

Yabagi ya caccaki batun sauya fasalin Naira
Kiyayya Ga Kasa Ne Yasa Aka Sauya Fasalin Naira, Inji Dan Takarar Shugaban Kasa | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Makiyan Najeriya ne suka kawo batun sauya kudin kasa

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Makiyin kasar nan ne kadai zai gabatar da irin wannan abu don kada a yi zabe ko kuma idan aka yi ma babu tabbacin za a yi na adalci, gaskiya kuma sahihin zane.”

Ya kuma bayyana cewa, wannan ne karon farko da yake ganin wata kasa a duniya da ta sauya fasalin kudadenta cikin makwanni biyu ba kacal.

Ya kara da cewa, wannan shiri na CBN ya durkusar da harkokin kasuwanci, kuma akwai bukatar daukar mataki nan kusa.

Yadda ya kamata a bi tsarin

A cewarsa, babban bankin ya kamata ya kai sabbin kudaden bankunan kasuwanci a fadin kasar kafin fara amfani dasu.

Da aka tambaye shi ko har tsawon wani lokaci ya kamata CBN ta dauka domin raba sabbin kudin da suka dace, ya ce bai sani ba, amma dai ya ce ya kamata lokacin ya fi wanda aka bayar a yanzu.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Babu laifin Buhari, Peter Obi ya ce 'yan Najeriya su hankalta, su yiwa Buhari uzuri

Ku yiwa Buhari uzuri, inji Peter Obi game da sabbin Naira

Batun Sani dai na zuwa kwanaki biyu bayan da dan takarar shugaban kasa na Labour, Peter Obi ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi hakuri su yiwa gwamnatin Buhari da CBN uzuri game sauyin kudade,

Ya bayyana cewa, sauyin kudi ba sabon abu bane a Najeriya, inda yace dama sabbin ka’idoji dole su zo da kunci, amma ba zai dauki tsawon lokaci ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel