Bankuna Sun Kulle Kofofinsu Yayin da Kwastomomi Ke Tsananin Bukatar Sabbin Naira a Legas

Bankuna Sun Kulle Kofofinsu Yayin da Kwastomomi Ke Tsananin Bukatar Sabbin Naira a Legas

  • An samu tsaiko a jihar Legas yayin da bankuna suka rufe kofofinsu ga kwastomomin da ke son cire kudi a ranar Talata
  • Wani daga cikin kwastomomi ya sharbi kuka yayin da ya bayyana halin da yake ciki na bukatar kudin jinyar matarsa
  • Ana samun mutanen da ke siyar da sabbin Naira yayin da wasu ke samun matsalar samun kudaden a bankunan Najeriya

Jihar Legas - Wasu bankuna a wasu yankunan jihar Legas sun ki bude kofofinsu ga kwastomomi a ranar Talata 7 Faburairu, 2023 saboda yadda jama'a suka yi cincirindo domin cire kudi ko sauya tsoffin kudi.

Daya daga cikin bankuna, an ce ya rufe kofarsa tun karfe 9 na safe domin kaucewa kwastomomin da za su shiga don cire kudi ko sakawa.

A yankin Obanikoro, wasu bankuna biyu sun rufe kofofinsu ga kwastomomi, inda aka ga wasu kwastomomin cikin fushi na kokawa tare da nuna bacin ransu.

Kara karanta wannan

Sauya Fasalin Naira: Kashi 80% Na Masu Sana'ar POS Sun Kare, Kungiyar Masu POS

Bankuna sun rufe kofa, sun hana kwastomomi shiga
Bankuna Sun Kulle Kofofinsu Yayin da Kwastomomi Ke Tsananin Bukatar Sabbin Naira a Legas | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Wasu daga ciki, sun zargi babban bankin CBN da hukumomin gwamnati da kitsa yadda ‘yan Najeriya za su kauracewa zaben 2023 da ke tafe nan da kwanaki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An yi rikici a bakin banki

An samu aukuwar wata ‘yar kitimurmura a wani bankin, inda aka ga wani mutum ya fito fili yana kukan rasa hanyar da zai samu don cire kudadensa.

Ya bayyana cewa, yana bukatar cire kudin ne domin biyan kudin jinyar matarsa da ke kwance a asibiti.

Ana musayar kudi ta hanyoyi masi ban mamaki

A wasu bangarorin Najeriya, an ga lokacin da wasu mutane ke siyar da sabbin kudade a kan farashin da ya saba ka’ida, lamarin da ya jawo cece-kuce.

An ga wata mata na musayar kudi, ta karbi N60,000 don ba da sabbin Naira na N50,000 ga wani attajiri da ya tura mata kudi ta banki.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Yadda Masu POS Suka Koma Siyan Kudi Daga Gidajen Mai a Wata Jihar Arewa

Jama’ar kasa sun daura laifin musayar kudi da kudi a mabambantan darajoji ga yadda gwamnan CBN ya kawo sabbin ka’idojin kudi a Najeriya.

Ka kawo mafita ga matsalar karancin Naira, sanata ga Buhari

A bangare guda, sanata daga jihar Kogi, Smart Adeyemi ya shawarci Buhari da ya tashi tsaye don tabbatar da an samu wadatuwar sabbin kudi a kasar.

Ya ce, kwanaki bakwai da shugaban ya dauka don warware damuwar sun yi kadan, akwai bukatar ya kawo mafita cikin kankanin lokaci.

Ya bayyana cewa, ‘yan Najeriya na mutuwa da shiga damuwa saboda karancin sabbin kudi da ake fama dashi a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel