Sauya Fasalin Naira: Kashi 80% Na Masu Sana'ar POS Sun Kare, Kungiyar Masu POS

Sauya Fasalin Naira: Kashi 80% Na Masu Sana'ar POS Sun Kare, Kungiyar Masu POS

  • Yan Najeriya sun shiga wani irin hali sakamakon rashin tsabar kudi cikin al'umma tun bayan fitowar sabbin kudi
  • Yayinda wasu ke kukan masu sana'ar POS na zaluntar al'umma, wasu sunce an kashe musu kasuwa
  • Kotun kolin Najeriya ta yanke hukuncin cewa a cigaba da amfani da tsaffin kudade daga yanzu zuwa karshen shekara

Kungiyar masu bankunan gida da wakilan bankuna watau Association of Mobile Money and Bank Agents in Nigeria (AMMBAN) ta bayyana cewa sama da kashi 80% na mambobinta sun karye.

Hakan ya faru ne sakamakon karancin Naira da ake fama da shi a fadin kasar, rahoton TheCable.

POS Guy
Sauya Fasalin Naira: Kashi 80% Na Masu Sana'ar POS Sun Kare, Kungiyar Masu POS
Asali: Facebook

Shugaban tantancewa na kungiyar, Hussein Olanrewaju, ya bayyana cewa karancin Nairan da ake fuskantan ya talauta masu sana'ar POS a fadin kasa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Naira: El-Rufa'i Da Yahya Bello Sun Dira Kotun Koli Inda Za'a Yanke Hukunci Yanzu

A cewarsa:

"Abin a fili yake kowa na gani, ana yiwa yan POS bita da kulli duk da cewa suna saukaka rayuwar kudi ga yan Najeriya marasa asusun banki da kuma wadanda ke da nisa da banki."
"Wasu yan POS din na fito da wasu dabaru na samun kudi wanda hakan ke tilastasu daura nauyin kan kwastamomi. Abin da ban takaici."
"Wannan ya sa kashi 80% na masu POS sun karye a fadin kasar kuma hakan na shafan rayukansu."
"Wuraren da za kaga yan POS 10 a baya, yanzu da wuya ka samu mutum biyu. Muna tattaunawa da CBN kan ta tsame yan POS daga karkashin bankuna kuma su zama masu cin gashin kansu don a kawo karshen wannan abu."

Rahotanni sun gabata kan yadda yan POS ke tafka haraji kan duk wanda ke da bukatar cire kudi.

A Abuja, Legit ta samu labarin cewa mutum na bada kashi 10% na adadin kudin da yake da niyyar cira.

Kara karanta wannan

Wa ya kaiku: Yadda aka maka matasa a kotu saboda fasa kofar Shoprite a wata jiha

Misali idan mutum na son karbar N10,000, sai ya bada dubu daya.

AMMBAN ta yi Alla-wadai ne wannan abu da mambobinta ke yi kuma ta gargade su bisa yin hakan.

Sauya Fasalin Naira Ya Rage Laifin Garkuwa da Mutane da Kuma Rashawa, Malami

A wani labarin kuwa, Antoni Janar na tarayya kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, yace sauya fasalin Naira da babban bankin Najeriya CBN tayi ya rage matsalar garkuwa da mutane a kasa.

Malami, a wata hira da yayi a gidan Radio Nigeria Kaduna, tace akwai alkhairai da babu wanda ke magana a kai, rahoton DailyTrust.

Asali: Legit.ng

Online view pixel