Canjin Kudi: Buhari Ya Fasa Yin Zama da Gwamnoni Bayan Sun Kai Kara a Kotu

Canjin Kudi: Buhari Ya Fasa Yin Zama da Gwamnoni Bayan Sun Kai Kara a Kotu

  • Da alama Shugaban kasar Najeriya da Gwamnonin jihohi ba za su yi taronsu na yau a Aso Rock ba
  • Babu tabbacin abin da ya jawo aka janye zaman, amma ana zargin karar da aka shiga a kotu ne
  • Muhammadu Buhari ya hadu da Shugaban kungiyar Gwamnoni da Shugaban Gwamnonin APC

Abuja - Zaman da aka shirya za ayi tsakanin Shugaban Najeriya da Gwamnonin jihohi a ranar Talata, 7 ga watan Fubrairu 2023, ba zai yiwu ba.

A rahoton Punch, mun ji labari cewa a farkon makon nan ne aka tsara cewa Mai girma Muhammadu Buhari zai yi wani zama da Gwamnoni.

Tattaunawar za ta shafi maganar tsarin canjin kudi da babban bankin Najeriya na CBN ya fito da shi.

A ranar Litinin wani babban jami’in fadar shugaban kasa ya shaida cewa Gwamnonin jihohi za su yi zama da Muhammadu Buhari a yau.

Kara karanta wannan

Masu Tunanin Akwai Wani Sabani Tsakanina da Buhari Za Su Ji Kunya Inji Tinubu

Ana haka kurum sai ga rahoto cewa an janye wannan taro da aka yi niyya, kuma majiyar fadar shugaban kasar ba ta iya bayyana wani dalili ba.

Buhari ya zauna da Tambuwal, Bagudu

A maimakon ya hadu da Gwamnoni 36 kamar yadda aka tsara, sai ga rahoto daga gidan talabijin Arise cewa an ga Gwamnoni biyu a Aso Rock.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Buhari
Shugaba Buhari a Aso Rock Hoto: @BuhariSallauOnline
Asali: Facebook

Gwamnonin nan su ne Aminu Bello Tambuwal wanda shi ne shugaban kungiyar Gwamnoni da shugaban Gwamnonin APC, Atiku Abubakar Bagudu.

Gwamnoni sun kai kara a kotu

A kaulin da aka fitar a Tribune, an ji an fasa yin wannan zama ne saboda wasu sun je kotu, sun yi nasarar haramtawa gwamnati kara wa’adin canjin kudi.

Majiyar fadar shugaban kasar ta ce shugaba Buhari yana tsoron ayi wa dokar kasa hawan kawara.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa Sun Aikawa Shugaban Kasa Buhari Muhimmin Sako a Kan Shirin Zabe

Zuwa yanzu babu tabbacin abin da shugaban na Najeriya ya tattauna da Gwamnonin jihohin na Sokoto da Kebbi da ya rufe labule da su a ofishinsa.

Sauran wadanda su ka hadu da shugaban kasar su ne; Gwamnan babban bankin CBN, Godwin Emiefele, da shugaban EFCC, AbdulRasheed Bawa.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha da Farfesa Ibrahim Gambari su na wajen tattaunawar. An hangi shugaban hafsoshin tsaro na kasa.

Emefiele ya je Aso Rock

A yau aka samu rahoto Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da gwamnan CBN a kan karancin sababbin Nairori da aka fito da su kwanan nan.

Bayanai sun fito game da zaman manyan kusoshin yau a fadar shugaban kasa a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel